Yadda Aka Kashe 'Yan Bindiga 40, Aka Kama Miyagu 916 a Jihar Katsina
- Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama mutum 916 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban a shekara guda
- CP Aliyu Musa, ya bayyana cewa an ceto mutane 319 da aka yi garkuwa da su tare da kwato dabbobi 2,081 da aka sace
- Rundunar ta kuma nakasa ayyukan ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, inda aka gurfanar da wasu a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Musa ya bayyana nasarorin da rundunar ta samu wajen yaki da laifuffuka a jihar cikin shekara guda.
Da yake jawabi a taron kammala shekara na 2024, ya ce rundunar ta samu nasarar da ba a taba ganin irinsa ba wajen kare rayuka da dukiyoyi a jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kwamishinan ya jinjina wa sadaukarwa da jarumtar jami’an sa wajen tabbatar da tsaro da doka a jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2024: An kashe 'yan bindiga 40 a Katsina
CP Aliyu Musa ya ce sun samu nasarar dakile kungiyoyin 'yan ta'adda da dama tare da kwato kayayyaki masu yawa da aka sace.
Haka zalika ya ce sun kama mutane 916 da ake zargi da laifuffuka, an ceto mutane 319 daga hannun masu garkuwa da mutane.
PM News ta wallafa cewa kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta kashe ‘yan bindiga 40 tare da kawo saukin zaman lafiya ga al’umma.
Kama barayin shanu da 'yan kwaya
Rundunar ta bayyana cewa ta kwato dabbobi 2,081 da aka sace tare da dawo da su ga masu su, abin da ya bunkasa tattalin arzikin karkara.
Haka zalika, 'yan sanda sun kama masu fashi da makami 199, sun gurfanar da manyan masu safarar miyagun kwayoyi 23 a gaban kotu.
An kama barayin mota 89 a Katsina
Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ta cafke masu satar motocin hawa 89 tare da kwato motoci fiye da 27.
Haka zalika, jami’an ‘yan sanda sun cafke mutane 573 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban, ciki har da bata gari da ke tayar da hankali ga zaman lafiya a jihar.
An kashe babban dan bindiga a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wani kasurgumin dan ta'adda a Katsina.
Legit ta rahoto cewa dan bindigar da aka kashe mai suna Alhaji Mo'oli ya fitini yankunan jihar Katsina da sace sacen dukiya da mutane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng