‘Bai Kamata ba’: Malamin Musulunci Ya Fusata da Aka Tsinewa Tinubu a Kasar Nijar

‘Bai Kamata ba’: Malamin Musulunci Ya Fusata da Aka Tsinewa Tinubu a Kasar Nijar

  • Yayin da alaka ke kara tsami tsakanin Najeriya da Nijar, wani malamin addinin Musulunci ya tsokaci kan lamarin
  • Sheikh Abubakar Malami ya nuna takaici yadda yan Nijar suke tsinewa Bola Tinubu da Najeriya saboda a tsakaninsu
  • Malamin ya ce bai kamata yan Najeriya su goyi bayan haka ba saboda suna da sabani da Bola Tinubu a wani bangare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Wani malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Malami ya yi magana kan sabanin da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

Malamin ya koka kan yadda yan Nijar suke tsinewa Bola Tinubu da Najeriya saboda zargin da ake yi masa.

Malamin Musulunci ya soki yan Nijar kan tsinewa Tinubu da Najeriya
Sheikh Abubakar Malami ya koka kan tsinuwar da yan Nijar suka yi wa Tinubu da Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Getty Images

Malamin Musulunci ya soki yan Nijar

Shehin malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Tinubu bai dace da Najeriya ba': Hadimin Osinbajo ya fadi mai nagarta da zai kawo sauyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, malamin ya ce rashin adalci ne su tsinewa Tinubu da Najeriya saboda kungiyar ECOWAS ba Najeriya kadai ba ce.

Ya shawarci yan Najeriya su rika adalci saboda don suna da sabani da Tinubu bai kamata su rika cewa Ameen ba kan tsinuwar da yan Nijar ke yi masa.

"Akwai sabani mai tsanani tsakanin Najeriya da Nijar saboda wannan dan dimukraɗiyya ne shi kuma soja ne."
"A kungiyar ECOWAS, shugaban kasar Najeriya shi ne jagora, Tinubu zai yi magana ne a madadin kasashen kungiyar ba Najeriya ba."
"Mu yi adalci, shin ya kamata yan Nijar za su tsinewa Tinubu da Najeriya amma ba su tsinewa Ghana da sauran kasashe ba?"
"Amma jama'a sun taru suka tsinewa Tinubu da yan Najeriya, mu kuma saboda sabani da Tinubu muna cewa Ameen."

- Sheikh Abubakar Malami

Nijar: Sheikh Albaniy ya shawarci yan Najeriya

Kun ji cewa malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya soki zarge-zargen da Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani ya yi.

Kara karanta wannan

"Ba mu son wa'azinku": Sanusi II ya fadawa kasashen Yamma abin da Arewa ke bukata

Malamin ya ce Tchini zai iya yin kuskure saboda shi ba mala'ika ba ne ko wani Annabi da komai ya fada gaskiya ne.

Wannan na zuwa ne bayan Tchiani ya zargi Najeriya da hada baki da Faransa domin kassara kasarsa ta Nijar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.