'Ya Yi Fice: Obasanjo Ya Bukaci Shugabanni Su Yi Koyi da Marigayi Tsohon Shugaban Kasa

'Ya Yi Fice: Obasanjo Ya Bukaci Shugabanni Su Yi Koyi da Marigayi Tsohon Shugaban Kasa

  • Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci shugabanni su yi koyi da salon shugabancin marigayi Jimmy Carter
  • Obasanjo ya yabawa tsohon shugaban Amurka bisa nasarorin da ya samu wajen kawo zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Masar
  • Ya kuma bayyana cewa Carter ya zama abin koyi wajen jagoranci, musamman kan jin kai, hakuri, da kawo karshen matsaloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ba shugabannin Najeriya shawara kan shugabanci nagari.

Obasanjo ya bukaci shugabannin siyasa na kasar su koyi darussa daga rayuwa da salon shugabancin marigayi Jimmy Carter.

Obasanjo ya ba shugabannin Najeriya shawara kan shugabanci
Olusegun Obasanjo ya shawarci shugabanni su yi koyi da tsohon shugaban Amurka. Jimmy Carter. Hoto: Olusegun Obasanjo.
Asali: Getty Images

Olusegun Obasanjo ya yabawa marigayi Carter

Obasanjo ya bayyana Carter a matsayin wanda ya nuna kaskantar da kai da daukar nauyi a lokacin mulkinsa, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan rasuwar tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter wanda ya rasu a gidansa da ke Georgia a ranar Lahadi yana da shekara 100.

Kara karanta wannan

"Carter mai son cigabanmu ne," Tinubu ya yi jimamin mutuwar tsohon shugaban Amurka

Tsohon shugaban Najeriya ya jinjina wa yadda Carter ya yi amfani da iko wajen kawo cigaba, Premium Times ta ruwaito.

Ya ce Carter ya yi fice wajen kawo zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Masar, da kuma fahimtar rikicin Falasdinawa da Isra’ilawa.

“Jimmy Carter mutum ne da ya fahimci iko, amma ya kuma fahimci cewa amfani da iko yana da alhakin da ke tattare da shi."
“Ya kaskantar da kai, kuma ya san yadda ake amfani da iko, idan ka karanta littafin da Carter ya rubuta kan rikicin Falasdinawa da Isra'ilawa, za ka fahimci yadda ya gane matsalar."

- Olusegun Obasanjo

Cif Obasanjo ya bukaci koyi da marigayi Carter

Bugu da ƙari, Obasanjo ya yaba wa Carter bisa sadaukarwar da ya yi bayan mulkinsa wajen ayyukan jin kai, kare hakkin dan adam, da goyon bayan dimokuradiyya.

Ya bayyana cewa salon shugabancinsa ya zama abin koyi ga shugabannin Najeriya da na duniya.

Kara karanta wannan

Tchiani: An samu bayanai daga kasar waje kan zargin Najeriya da hada kai da Faransa

Obasanjo ya gano matsalar Najeriya

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nuna damuwarsa kan tarin kalubale da matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Olusegun Obasanjo ya dora alhakin matsalolin da suka addabi kasar nan a kan shugabanni da kuma mabiyansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.