Yadda Kauyuka 50 Suka Watse da Turji Ya Yi Barazana, Jigon APC Ya Shawarci Tinubu
- Fargaba ta mamaye jihar Zamfara yayin da fiye da kauyuka 50 suka zama kufai a Shinkafi sakamakon barazanar fitaccen ɗan bindiga, Bello Turji
- Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare a kananan hukumomi uku idan ba a saki yan uwansa da sojoji suka kama ba
- Rahotanni sun bayyana cewa fiye da kashi 80% na mazauna Shinkafi sun tsere zuwa Kauran-Namoda don tsira daga hare-haren Turji
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Tsoron rashin tsaro ya mamaye garuruwan Zamfara yayin da aka sanar da cewa fiye da kauyuka 50 a yankin karamar hukumar Shinkafi sun zama kufai.
Wannan hijira ta faru ne sakamakon tsoron barazanar da dan bindiga, Bello Turji ya yi ga kauyukan.
Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare
Jigon APC, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a Gusau, cewar jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan bidiyon da Bello Turji inda ya gargadi hukumomi cewa zai kai hari a Shinkafi, Zurmi, da kuma Isah, idan ba a saki ɗan uwansa, Bala Wurgi, da aka kama ba.
Ya yi wannan barazana ne a ranar Larabar 25 ga watan Disambar 2025 da ta gabata, yana mai cewa lokaci yana ƙurewa kafin ƙarshen shekara.
Mazauna kauyukan Zamfara sun bar gidajensu
Dr. Sani Abdullahi ya ce tun bayan fitar bidiyon Turji, fiye da kauyuka 50 a Shinkafi sun zama kufai.
Ya ƙara da bayyana cewa fiye da kashi 80% na mazauna yankin sun koma garin Kaura-Namoda don samun tsaro, cewar Punch.
Ya bayyana wannan barazana a matsayin wulakanci ga jami'an tsaro na Najeriya kuma ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin gaggawa.
“Wannan barazana kai tsaye ce ga tsaron ƙasa, ina kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rundunar soji su ɗauki matakin kare rayukan al’umma daga waɗannan hare-haren da ake shirin kai wa.”
- Sani Abdullahi
Wannan matsalar hijira ta nuna yadda rashin tsaro ya ƙara muni a yankin, inda al'umma ke kira ga gwamnati ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Sojoji sun kama bai aikawa Turji makamai
Kun ji cewa Rundunar sojojin 'Operation Fansar Yamma' ta kama wata mata mai shekaru 25 da ake zargin tana safarar bindigogi da alburusai 764 zuwa ga ƴan fashi.
Kakakin sojoji ya bayyana cewa an kama matar da wani abokin tafiyarta ne a Badarawa, karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng