'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Manyan Malamai a Jihar Adamawa

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Manyan Malamai a Jihar Adamawa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da malaman coci guda biyu a jihar Adamawa ranar Lahadin da ta gabata
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen Adamawa, SP Suleiman Naguroje ya ce an tura dakaru domin ceto fastocin cikin koshin lafiya
  • Shugaban cocin EYN, Rabaran Daniel Mbaya ya buƙaci ƴan Najeriya su taimaka masu da addu'o'i don Allah ya kubutar da malaman

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Adamawa ta tabbatar da sace malaman coci guda biyu.

Yan sandan sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da limamin cocin 'Eklesiyar Yan’uwa a Nigeria' (EYN), Rabaran James Kwayang da sakatarensa, Rabaran Ishaku Chiwar.

Yan sanda.
Wasu miyagu sun sace fastocin cocin EYN guda 2 a jihar Adamawa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan sanda sun tabbatar da sace malamai

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ne ya tabbatar da sace manyan limaman cocin ga jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Direba ya sha giya ya afka gidan mutane, ya jawo gobara a gidaje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suleiman Nguroje ya bayyana cewa tuni rundunar ‘yan sandan ta tura jami’anta domin ceto limaman cocin biyu daga hannun waɗanda suka sace su.

Mahara sun sace limaman cocin EYN da ke garin Mbila- Malibu ranar Lahadi da misalin karfe 11 na dare a karamar hukumar Song ta jihar Adamawa.

Matakin da cocin EYN ta ɗauka

Shugaban EYN, Rabaran Daniel Mbaya wanda ya tabbatar da lamarin, inda ya yi kira ga jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa don ganin an sako fastocin lafiya.

Ya bukaci malaman addini, ƴan majami’ar EYN da ‘yan Najeriya baki ɗaya su taimakawa cocin da addu’o’i domin fastocin da aka sace su kubuta cikin ƙoshin lafiya.

A rahoton Daily Post, Rabaran Daniel ya ce:

"Muna kira ga ƴan Najeriya da mabiya cocin EYN su tama mu dabaddu'o'in Allah ya kubutar da waɗannan mutane biyu kuma ya ba iyalansu karfin jure wannan hali.
"Wannan lamari dai ya tayar da hankulan jama’a da mabiya cocin EYN, don haka muna rokon addu’o’in ku da goyon bayanku a wannan mawuyacin lokaci.”

Kara karanta wannan

An yi arangama tsakanin ƴan sanda da masu garkuwa a Kwara, an ceto mutane 13

Ƴan sanda sun ceto mutum 13 a Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an ƴan sanda sun samu nasarar ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su a jihar Kwara.

Gwarazan ƴan sandan sun yi gumurzu da masu garkuwa da mutanen kafin su yi nasarar dawo da waɗanda aka sace gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262