Direba Ya Sha Giya Ya Afka Gidan Mutane, Ya Jawo Gobara a Gidaje

Direba Ya Sha Giya Ya Afka Gidan Mutane, Ya Jawo Gobara a Gidaje

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Jigawa sun ce wata mota ta afka wa gida a Dutse, lamarin ya jawo gobara da ta kone gidaje huɗu
  • Bayanan da rundunar 'yan sanda ta fitar sun nuna cewa wata mata da yara sun tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku
  • Kakakin 'yan sandan jihar ya tabbatar da cewa jami'ansu sun kama mutane guda biyu da ake zargi suna cikin maye suka tuka motar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - A cikin wani hatsari mai cike da firgici, mota ta afka wa wani gida a unguwar Elpies Street, Mobile Quarters Dutse, a safiyar ranar 29 ga Disamba, 2024.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wata mata da yaranta da ke barci a cikin ɗakin sun tsallake rijiya da baya a hatsarin.

Kara karanta wannan

An yi arangama tsakanin ƴan sanda da masu garkuwa a Kwara, an ceto mutane 13

Hadarin Jigawa
Mota ta afka gida a Jigawa. Hoto: Lawal Shiisu Adam
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya bayyanawa Legit cewa an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a hatsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin hatsarin mota a jihar Jigawa

Punch ta wallafa cewa hatsarin ya faru ne lokacin da wata mota kirar Toyota Corolla mai lambar NSR 120 BC ta afka cikin gidan da ke Elpies Street, Mobile Quarters Dutse.

An ce Muhammad Galadima, mai shekara 32 ne mamallakin motar, amma ya ba Abdullahi Abubakar Sadiq, mai shekara 41 tuki, wanda ya amsa ba tare da kwarewa a tukin mota.

Yayin da hatsarin ya faru, motar ta rusa katanga ta shiga cikin ɗakin da mata da yara ke barci, kafin ta haddasa gobarar da ta shafi gidaje uku na makwabta.

Matakin gaggawa da aka ɗauka

Rundunar ‘yan sanda ta ce bayan samun rahoton hatsarin, jami’anta tare da ma’aikatan kashe gobara da goyon bayan wasu mazauna unguwar sun yi nasarar kashe wutar.

Kara karanta wannan

An tsinci gawarwaki bayan mummunan hatsarin mota, mutane 13 sun kone kurmus

Bayanai sun tabbatar da cewa ba a rasa rai ba a hatsarin, amma an samu asarar dukiyoyi masu yawa sakamakon gobarar da ta ƙone gidaje huɗu ƙurmus.

Masu laifi sun shiga hannun 'yan sanda

DSP Lawan Shiisu Adam ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wadanda ake zargi guda biyu tare da motar, kuma ana gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Kasancewar ana zargin hadarin ya faru ne dalilin maye da direban ke ciki, an gargadi mutane da su guji shaye-shaye da gudanar da ayyukan da ka iya jawo hatsari da cutar da jama’a.

Hadari ya kashe mutane 13 a Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar FRSC a jihar Ondo ta sanar da cewa mutane 13 sun rasu a wani hatsarin mota a hanyar Owo-Ikare Akoko.

Legit ta rahoto cewa wasu motoci biyu sun yi karo da juna kuma suka fara ci da wuta, lamarin da yawo mutane 13 suka kone kurmus.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng