Matatar Man Najeriya Ta Fara Aiki bayan Ta Fatakwal, da Yiwuwar Fetur Ya Ƙara Araha
- Matatar mai mai ƙarfin tace ganga 125,0000 da ke Warri ta gwamnatin Najeriya ta dawo aiki bayan tsawon lokaci
- Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Mele Kyari ya tabbatar da hakan yayin rangadin duba yanayin aikin yau Litinin
- Kyari ya ce galibin ƴan Najeriya na ganin hakan ba mai yiwuwa ba ne amma yanzu ga shi suna bai wa maraɗa kunya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta - Matatar man fetur mallakin gwamnatin Najeriya da ke Warri a jihar Delta ta kama aiki bayan tsawon lokaci.
Matatar Warri mai ƙarfin tace ɗanyen mai ganga 125, 000 a kowace rana ta dawo aiki makonni kalilan bayan gyara matatar Fatakwal.
Shugaban kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL, Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin rangadin duba aikin gyaran matatar ranar Litinin, Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya tabbatar matatar Warri ta fara aiki
Kafin fara rangadin duba aikin, an ji shugaban NNPCL na yi wa tawagarsa jawabi da cewa:
"Za mu shiga da ku cikin wannan wuri, wannan matata ta fara aiki duk da dai ba a gama aiki 100% ba amma dai saura ƙiris, muna kan aiki har yanzu.
"Galibin mutane na tunanin waɗannan abubuwan ba gaskiya ba ne, suna ganin ba za ta taɓa yiwuwa ba, muna so ku gani kuma ku tabbatar da gaske ne."
Daga cikin tawagar akwai babban jami’i/shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA), Farouk Ahmed.
Matatar Warri ta bi sahun ta Fatakwal
Wannan ci gaban na zuwa ne makonni bayan kamfanin NNPCL ya tabbatar da kammala gyaran matatar Fatakwal a jihar Ribas.
A yanzu dai matatar Warri ta dawo aiki, inda ake ganin wannan zai ƙara haifar da gasa a kasuwar fetur kuma ana hasashen watakila hakan ya zama alheri ga ƴan Najeriya.
Ɗangote ya faɗi dalilin rage farashin fetur
A wani rahoton, an ji cewa shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote ya bayyana cewa yanayin kasuwa ne ya janyo rage farashin man fetur zuwa ƙasa da N900.
Hamshakin ɗan kasuwar, Alhaji Aliko Ɗangote ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi kwanaki kaɗan bayan matatarsa ta yi wa ƴan kasuwa rangwame.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng