Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wankin Babban Bargo ga Gwamnan Bauchi kan Haraji
- Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare ya soki kalaman Gwamna Bala Mohammed kan haraji
- Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwa kan furucin da gwamnan ya yi na cewa za su nuna wa Tinubu hakikanin halinsu
- Sunday Dare ya nemi gwamnan Bala Mohammed da ya janye kalaman da ya yi kuma ya mayar da hankali kan ci gaban jiharsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan kalaman Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, dangane da kudirin gyaran haraji.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya bayyana cewa irin wadannan kalamai ba su dace su fito daga gwamna ba.
Sunday Dare ya yi wannan bayani ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya yi tir da furucin gwamnan da ya ce, “Za mu nuna wa shugaba Tinubu asalin halinmu.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta wallafa cewa hadimin shugaban kasar ya ce kalaman sun saba wa tsarin tattaunawa da ake bukata tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya.
Dare: Gwamnatin Bauchi ta karɓi tallafi sosai
Sunday Dare ya bayyana cewa gwamnatin Bauchi ta karɓi Naira biliyan 144 daga asusun tarayya a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, adadin da ya ninka rabon da ta saba samu a baya.
Sai dai duk da karin kudin, Dare ya ce jihar na fama da matsalolin da suka hada da talauci, wanda ya kamata a mai da hankali wajen magance su, maimakon yin barazana ga gwamnatin tarayya.
Dare ya bukaci gwamna ya janye kalamansa
Mai magana da yawun shugaban kasar ya nemi gwamna Bala Mohammed da ya janye kalamansa, yana mai cewa wannan ba shi ne muradin yankin Arewa ba.
“Arewa tana fatan samun hadin kai da tattaunawa mai ma’ana tare da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da kasa ke fuskanta,”
- Sunday Dare
Dare ya ja hankalin gwamnan da ya maida hankali kan tattaunawa domin magance duk wani ƙorafi kan kudirin haraji maimakon barazana.
Gwamnan Bauchi ya gana da abokansa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi ya shirya gagarumar liyafa ga abokansa da suka kammala firamare tare a shekarun baya.
Sanata Bala Mohammed da abokansa sun kammala karatun firamare a shekarar 1971 wanda hakan ke nuna cewa sun shafe sama da shekaru 50 da gamawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng