Tchiani: An Samu Bayanai daga Kasar Waje kan Zargin Najeriya da Hada Kai da Faransa

Tchiani: An Samu Bayanai daga Kasar Waje kan Zargin Najeriya da Hada Kai da Faransa

  • Jama'ar yankunan kan iyakar Najeriya sun musanta zargin shugaban sojin Nijar, Abdurrahman Tchiani na cewa ana shirin lalata kasarsa
  • Haka zalika wasu masana da shugabanni sun bayyana zargin da Abdurrahman Tchiani ya yi a matsayin marasa tushe da shaida
  • Hafsun tsaron kasar Côte d’Ivoire ya yi bayanai kan zarge zargen da Tchiani ya yi kuma ya bayyana matakin da ya kamata a dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasar Nijar, Abdurrahman Tchiani, ya sha caccaka daga al’ummomi da shugabanni a kan zarge-zargen da ya yi wa gwamnatin Najeriya.

Janar Tchiani ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Nijar cewa akwai wani sansanin sojin Faransa a wani daji mai suna Gaba da ke Sokoto a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya soki El Rufa'i kan zargin kabilanci a gwamnatin Tinubu

Nijar
An caccaki shugaban Nijar kan zargin Najeriya. Hoto: Côte d’Ivoire
Asali: Getty Images

Daily Trust ta rahoto cewa shugabanni da mazauna yankunan kan iyakar sun musanta wadannan zarge-zargen, suna masu cewa babu wani sansanin sojin ƙasashen waje a Sokoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’ar iyakokin Najeriya sun karyata Tchiani

Wani jagoran al’umma a Illela, Sarkin Arewan Araba, Alhaji Abubakar Yusufu, ya tabbatar da cewa babu wani wuri mai suna Gaba a yankin sa, wanda ke kusa da iyakar Konni ta Nijar.

Sokoto na da iyaka da Nijar a kananan hukumomin Illela, Gada, Tangaza, Gudu, da Sabon Birni. Duk da haka, shugabannin yankunan sun ce babu wani sansanin sojin ƙetare a wuraren.

Masana sun karyata zargin shugaban Nijar, Tchiani

Masanin tarihi da harkokin tsaro a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Dr Murtala Rufa’i ya ce binciken sa kan iyakar Najeriya da Nijar ya tabbatar da cewa zargin Tchiani ba gaskiya ba ne.

Dr Rufa’i ya ce ya yi bincike a yankunan kan iyaka amma babu wani sansanin sojin Faransa a Sokoto.

Kara karanta wannan

Rarara ya yi wa shugaban Nijar wankin babban bargo kan zarginsa, ya tona asiri

Ya kara da cewa wannan zargi na Tchiani na iya zama yunƙuri ne na karkatar da hankali kan matsalolin cikin gida, musamman hare-haren da 'yan ta’adda suka kai kan bututun mai a Nijar.

An zargi Tchiani da nuna rashi kwarewa

Tsohon jakadan Najeriya, Ambasada Suleiman Dahiru, ya bayyana zargin Tchiani a matsayin mai nuna rashin kwarewa.

A cewarsa,

“Wannan zargi na Tchiani ya nuna rashin kwarewarsa, musamman a wannan zamanin kimiyya da fasaha.”

- Ambasada Suleiman Dahiru

Haka kuma, tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar Adamawa, Ahmed Sajo, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji aminta da irin wadannan zarge-zarge da Tchiani ke yi ba tare da wata hujja ba.

Bayanin hafsun tsaron Côte d’Ivoire

Hafsun tsaron kasar Côte d’Ivoire, Janar Lassina Doumbia ya ce zargin da Tchiani ya yi babu hujja a cikinsu kwata kwata.

Janar Lassina Doumbia ya bayyana cewa babban matakin da ya kamata kasashe su dauka shi ne inganta tsaro a yankunansu.

Kara karanta wannan

Bayan zargin shugaban Nijar, Sarakuna sun fadi gaskiya kan zargin a yankunansu

Sheikh Albani ya caccaki shugaba Tchiani

A wani rahoton, kun ji cewa malamin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Muhammad Adam Albani ya yi magana kan zargin shugaban Nijar.

Sheikh Albani ya bayyana cewa ba lallai ba ne a yarda da abin da Tchiani ya fada a kan hadin kan Najeriya da Faransa wajen cutar da Nijar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng