Kotun Shari'a: Fitaccen Basarake Ya Goyi bayan Kafa Kotunan Musulunci, Ya Jero Dalilai
- Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan kafa kotunan Shari'a, Basarake a yankin Yarabawa ya goyi baya
- Sarkin Iwo a jihar Osun, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya ce babu gwamnati da za ta hana Musulmai a Kudu maso Yamma amfani da dokar Shari’a
- Oba Akanbi ya jaddada cewa dokar Shari’a ta kasance cikin tsarin rayuwar Kudu maso Yamma sama da shekara 100
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Oluwo na Iwo a jihar Osun, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya goyi bayan shirin kafa kotunan Shari'ar Musulunci.
Oba Akanbi ya bayyana cewa babu wata gwamnati da za ta iya hana Musulmai a Kudu maso Yamma ‘yancin amfani da dokar Shari’ar Musulunci.
Basarake ya goyi bayan kafa kotun Shari'ar Musulunci
A wata hira da ya yi da The Punch, Oba Akanbi ya ce aiwatar da dokar Shari’a a Kudu maso Yamma ya dace da tsarin addini da al’adu na Musulmai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Basaraken ya ce wannan ‘yanci an tabbatar da shi a tsarin mulkin Najeriya, kuma yana cikin ‘yancin addini da kundin tsarin mulki ya ba kowanne dan kasa.
Ya kawo misalai da tsarin bankuna masu bin dokar Shari’a da kuma kwalejin Shari’a da ke Iwo, inda ya ce suna tabbatar da cewa rayuwar Musulmai ta samu kulawa ta musamman.
Har ila yau, basaraken ya ce dokar Shari’a ta fi mayar da hankali kan batutuwan gado, aure, da saki na Musulmai.
“Muna da bankunan Shari’a a Kudu maso Yamma, kuma suna aiki da dokokin Shari’a, dokar Shari’a tana Iwo tun fiye da shekara 100."
"Wannan ‘yancin Musulmai ne su zabi dokokin gargajiya ko na kotun gwamnati.”
- Oba Abdulrasheed Akanbi
'Bai shafi sauran addinai ba' - Oba Akanbi
Oba Akanbi ya kuma jaddada cewa dokokin Shari’a ba su shafi mabiya wasu addinai ba, cewar Tribune.
“Duk wanda ya ji yana son Shari’a, sai ya musulunta, ko Musulmi yana da ‘yancin canzawa zuwa Kiristanci.
"Kowa yana da ‘yancin yin addininsa, dokar Shari’a bai kamata ta zama matsala ga sauran addinai ba."
- Oba Abdulrasheed Akanbi
An dage shirin kafa kotunan Shari'ar Musulunci
Kun ji cewa Kungiyar Musulmin jihar Oyo ta ɗage bikin kaddamar da kotun shari'ar Musulunci da ta shirya ranar 11 ga watan Janairu, 2025.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce addinin Musulunci ya yi umarni da zaman lafiya don haka ta ɗage buɗe kotun sai baba ta gani.
Batun kaddamar da kotun dai ya fuskanci kalubale da suka daga mutane, wasu sun yi zargin hakan shirin Musuluntar da yankin ne.
Asali: Legit.ng