An Yi Arangama Tsakanin Ƴan Sanda da Masu Karkuwa a Kwara, An Ceto Mutane 13
- 'Yan sandan Kwara sun kubutar da mutane 13 da aka sace a wani ceton gaggawa da tai tare da hadin gwiwar jami'an Oke-Ero
- Rahoto ya nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun kwashin kashinsu a hannun jami'an tsaro lamarin da ya sa suka arce
- Wadanda aka ceto sun samu kulawa a asibiti sannan aka mayar da su cikin iyalansu kamar yadda rundunar 'yan sandan ta sanar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Rundunar ’yan sandan Kwara ta ceto mutane 13 da aka sace a wani aikin kai daukin gaggawa da ta kai a jihar.
Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Ilorin.
'Yan sanda sun kubutar da mutane 13
Ejire-Adeyemi ya ce wannan nasara ta nuna jajircewar rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar a cewar rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin 'yan sandan ya ce wani hadin gwiwa tsakanin ’yan sanda da ma’aikatan tsaron karamar hukumar Oke-Ero ne ya kai ga ceto wadanda aka sace.
Wadanda aka sace sun hada da mutane 13 da wasu mahara suka yi garkuwa da su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa biki a Kogi.
An mayar da mutanen ga iyalansu
Lokacin ceton, mahara shida da suka saka kayan soji sun yi musayar wuta da jami’an tsaro amma sun sha kashi tare da arcewa da raunuka.
Wadanda aka ceto sun hada da mata uku da maza 10 kuma sun fito daga yankuna daban-daban ciki har da Odo-Owa, Ilorin da Ogbomoso.
Bayan da aka basu kulawa a asibiti, an mayar da wadanda aka ceto gida cikin koshin lafiya kamar yadda sanarwar Ejire-Adeyemi ta nuna.
Shugaban ma'aikatan fadar Kwara ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar Prince AbdulKadir Mahe, shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Kwara a ranar Asabar.
Yayin da Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya yi jimamin mutuwar Prince AbdulKadir, an rahoto cewa an yi jana'izar jami'in a gidansa na Adewole Estate, Ilorin.
Asali: Legit.ng