Gwamnan Zamfara Ya Faranta Ran Ma'aikata Ana Shirin Bankwana da 2024
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince a ba ma'aikatan gwamnati albashin wata na 13
- Dauda Lawal ya amince a biya ma'aikatan kaso 30% na albashinsu a matsayin alawus na shekarar 2024 da ke bankwana
- Gwamnan ya buƙaci ma'aikatan da su ƙara nuna jajircewa da ƙwazo wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta sake jaddada ƙudirinta na kyautata jin dadin ma’aikatanta.
Gwamnatin ta Dauda Lawal ta amince da biyan alawus na ƙarshen shekara ga ma’aikatan gwamnati da ƴan fansho.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar da shugaban ma’aikatan jihar Zamfara, Ahmad Aliyu Liman ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dauda ya amince a ba ma'aikata alawus
Gwamna Dauda Lawal ya amince da biyan albashin wata 13 kwatankwacin kashi 30% na albashin ma’aikata a matsayin alawus na shekarar 2024.
Shirin dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na tabbatar da shugabanci na gari da ƙara ƙarfafa gwiwar ma'aikata.
Za a ba da kuɗin ba kawai ga ma'aikatan gwamnati ba har ma da masu karɓar fansho, wanda ke nuna jajircewar gwamnatin wajen faranta ran ma'aikatanta.
"A ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da shugabanci nagari, Gwamnan Dauda Lawal PhD ya sake amincewa da biyan albashin wata na 13 wanda ya yi daidai da kaso 30% na albashi a matsayin alawus na ƙarshen shekarar 2024.
"Wannan ƙarin ba wai kawai ga ma'aikata ne kaɗai ba, har da masu karɓar fansho."
- Ahmad Aliyu Liman
Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci dukkan ma’aikatan gwamnati da su yaba da abin da gwamnatin ta yi musu, ta hanyar nuna ƙara jajircewa da aiki tuƙuru.
Gwamnan Oyo zai fara biyan albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta sanya lokacin fara biyan mafi ƙarancin albashi.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya bayyana cewa gwamnatin za ta fara biyan mafi ƙarancin albashin a watan Janairun 2025 bayan ta cimma matsaya da ƴan ƙwadago.
Asali: Legit.ng