Sojojin Sun Fafafa da 'Yan Bindiga, an Rasa Rayukan Jami'an Tsaro

Sojojin Sun Fafafa da 'Yan Bindiga, an Rasa Rayukan Jami'an Tsaro

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da ƴan bindiga da ake zargin na ƙungiyar ESN ne a jihar Imo
  • A yayin arangamar an rasa rayukan jami'an sojoji guda biyu yayin da aka nemi wani guda ɗaya sama ko ƙasa aka rasa
  • Daga baya sojoji sun bi sahun ƴan bindigan inda suka kashe ɗaya daga cikinsu tare da ƙwato makamai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Rundunar sojojin Najeriya ta ce an kashe sojoji biyu tare da ɓatan guda ɗaya bayan sun fafata da ƴan bindigan da ake zargin ƴan ƙungiyar ESN ne.

Sojojin sun bayyana cewa an yi arangamar ne a ƙauyen Osina da ke ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a jihar Imo.

'Yan bindiga sun hallaka sojoji a Imo
'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Joseph Akubo, kakakin runduna ta 34 Artillery Brigade, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'addan ISWAP sun sheke tsageru masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ESN mai ɗauke da makamai wani reshe ne na masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB).

Sojoji sun fafata da ƴan bindiga

Joseph Akubo ya bayyana cewa faɗan ya auku ne a ranar Juma’a lokacin da sojoji suka amsa kiran da aka yi musu game da harin da mayaƙan IPOB/ESN, a lokacin da suke dawowa daga sintiri na yau da kullum.

"Ƴan bindigan waɗanda aka mamaya, sun tsere cikin ruɗani."
"Abin takaici, an kashe jami’an tsaro guda biyu a yayin fafatawar sannan wani guda ɗaya ya ɓace. Ƴan ta’addan sun ƙwace makamansu da suka hada da bindiga ƙirar AK-47 da barkonon tsohuwa."

- Joseph Akubo

Ya ce an ɗauko gawarwakin sojojin yayin da jami'an tsaro suka bi bayan maharan da suka tsere.

Akubo ya ƙara da cewa daga baya sojojin sun tare waɗanda ake zargin mayaƙan ne a ƙauyen Nkwachi, inda suka yi musayar wuta.

"A yayin wannan artabu, an kashe ɗaya daga cikin ƴan bindigan, yayin da wasu suka gudu zuwa cikin dajin da ke kusa. An samu nasarar kwato bindiga ƙirar AK-47."

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun yi kwanton bauna kan 'yan bindiga, sun tura tsageru barzahu

- Joseph Akubo

Sojoji sun kashe ƴan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta kan maɓoyar ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Sojojin a yayin harin sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa tare da lalata makamai da sauran kayan aiki na masu tayar da ƙayar bayan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng