Dakarun Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda, Sun Sheke Miyagu Masu Yawa

Dakarun Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda, Sun Sheke Miyagu Masu Yawa

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu tarin nasarori kan ƴan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan
  • Sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 148 tare da cafke wasu masu laifi 258 ciki har sa masu safarar makamai
  • Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ya bayyana cewa an kuma ceto mutanen da ƴan ta'adda suka yi garkuwa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a sassan daban-daban na ƙasar nan.

Dakarun sojojin da ke aikin samar da tsaro a faɗin ƙasar nan, sun kashe ƴan ta'adda 148 tare da cafke masu laifi 258 ciki har da masu safarar makamai mutum biyu.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo-Janar Edward Buba ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwa, ta kone shaguna masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe ƴan ta'adda

An kama masu safarar makaman masu suna Danweri da Abubakar Hamza a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi

Manjo Janar Edward Buba ya ce dakarun sojoji sun kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato makamai 146 da alburusai 2,599.

"Bindigogin da aka ƙwato sun haɗa da PKT guda biyu, AK47 guda 72, bindigogi guda 33, bindigu ƙirar gida guda 28, SMG na gida guda biyu, RPG guda ɗaya, bututun RPG guda ɗaya da jigida guda 39."
"Sauran sun haɗa da harsasai na musamman guda 1,596 masu kaurin 7.62mm special ammo, harsasan NATO guda 636 masu kaurin 7.62mm, harsasai guda 111 masu kaurin 7.62 x 51mm, harsasai guda 114 masu kaurin 7.62 x 54mm ammo, alburusai guda 25 masu kaurin 9mm."
"Sauran su ne manyan harsasai guda 98, rediyon baofeng guda uku, motoci uku, babura 36, wayoyin hannu 40 da tsabar kuɗi N1,838,000.00 da sauransu."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun fara amfani da jirage marasa matuka, DHQ ta tura sako ga 'yan Najeriya

- Manjo Janar Edward Buba

Sojoji sun cafke ɗan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar cafke wani ɗan ta'addan Boko Haram a jihar Taraba.

Gwarazan jami'an tsaron sun kuma cafke wani jami'in tsaro na ƴan banga wanda yake haɗa baki da masu garkuwa da mutane wajen ba su bayanai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng