An Tsinci Gawarwaki bayan Mummunan Hatsarin Mota, Mutane 13 Sun Kone Kurmus

An Tsinci Gawarwaki bayan Mummunan Hatsarin Mota, Mutane 13 Sun Kone Kurmus

  • Hukumar kiyaye hadura ta kasa, FRSC a Ondo ta bayyana cewa mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyar Owo-Ikare Akoko
  • Motoci biyu sun yi taho-mu-gama kuma suka kama wuta, inda mutane 13 suka kone kurmus a hatsarin
  • An kai wanda ya tsira asibiti, yayin da gawarwakin aka adana su a dakin ajiye gawa na Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Owo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Hukumar Kiyaye Hadura ta Tarayya (FRSC) reshen Ondo ta sanar da mutuwar mutane 13 a wani mummunan hatsarin mota.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a hanyar Owo-Ikare Akoko, kusa da kauyen Abule Panu a karamar hukumar Owo.

Mutane 13 sun kone kurmus a wani hatsarin mota
Hukumar FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane 13.a wani hatsarin mota a Ondo. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane

An ce motoci biyu ne suka yi taho-mu-gama sannan suka kama wuta, inda dukkan fasinjojin suka kone kurmus, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An farmaki wata maboyar gaggan barayi a Kano, an kwato kayan da suka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar FRSC a jihar, Dakta Samuel Ibitoye, ya ce hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 10:14 na safe, inda mutane 13 suka mutu a cikin motocin biyu.

“Jimillar mutane 14 ne hatsarin ya rutsa da su; daga cikinsu 13 sun kone kurmus, yayin da mutum ɗaya kawai ya tsira da mummunan rauni."
"An garzaya da wanda ya tsira zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Owo, yayin da aka kai gawawwakin dakin ajiye gawa na asibitin.”

- Samuel Ibitoye

FRSC ta ba fasinjoji da direbobi shawara

Samuel Ibitoye ya ce jami’ansa, tare da ‘yan sanda da hukumar kashe gobara ta jiha, sun isa wurin don ceto wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Sai dai mutum guda ne aka samu a raye daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su, inda ya shawarci direbobi su kasance masu hakuri a hanya, su kula da motocinsu.

Ya kuma shawarci fasinjoji su dinga sanar da tuki mai hatsari, yana mai jaddada cewa kiyaye hanya na da mahimmanci ga kowa, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ziyarci kauyuka 2 da jirgin sojoji ya jefa bama bamai kan bayin Allah

Tankar mai ta yi bindiga a Ondo

Kun ji cewa mutane da dama sun shiga tashin hankali bayan wani iftila'i da ya faru a jihar Ondo da yammacin ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024.

Hakan ya faru ne bayan wata tankar mai ta kife a bakin titi da ya yi sanadin tashin gobara mai ƙarfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.