'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini da Iyalansa, Sun Bukaci N75m

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini da Iyalansa, Sun Bukaci N75m

  • Wani limamin cocin Anglican a jihar Ondo ya faɗa hannun ƴan bindiga tare da iyalansa a makon da ya gabata
  • Miyagun ƴan bindigan sun sace malamin addinin na Kirista ne lokacin da yake tafiya tare da iyalansa a cikin mota
  • Ƴan bindigan sun kira waya inda suka buƙaci a ba su kuɗin fansa N10m kafin daga baya su ƙara zuwa N75m

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Ƴan bindiga sun sace wani limamin cocin Anglican mai suna Cannon Olowolagba tare da matarsa da ƴaƴansa guda biyu.

Hukumar tsaro ta Amotekun ta tabbatar da sace malamin addinin na Kirista a ranar.

'Yan bindiga sun sace malamin addini a Ondo
'Yan bindiga sun sace limamin cocin Anglican a Ondo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Ise Akoko-Iboropa a ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa maso Gabas ta jihar Ondo a ranar Lahadin da ta gabata.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bajinta, sun cafke masu laifi 859 a jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace malamin addini

A cewar wata majiya daga al’ummar yankin, limamin cocin tare da iyalan nasa suna tafiya ne a cikin mota, sai ƴan bindigan suka tare su a kan hanya sannan suka tafi da su zuwa cikin daji.

Sai dai, majiyar ta bayyana cewa ƴan bindigan sun tuntuɓi ƴan uwansa inda suka buƙaci a ba su kuɗin fansa naira miliyan 10 domin su sako mutanen.

Hakazalika, Bishop na cocin Anglican Diocese, Babajide Bada, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, ya ce masu garkuwa da mutanen sun ƙara kuɗin fansan zuwa Naira miliyan 75.

"Tun a wancan lokacin waɗanda suka yi garkuwa da su suke ta kiran waya. Sun don neman kuɗin fansa. Da farko suka ce Naira miliyan 10. Amma da muka tattara kuɗi don mu je a sake su, sai suka canza zuwa Naira miliyan 75. Shi ya sa har yanzu suke a tsare."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsaka da bikin Kirsimeti, sun hallaka bayin Allah

- Babajide Bada

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Kwamandan rundunar Amotekun a jihar, Akogun Adetunji Adeleye, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an ceto su.

“Gaskiya ne, duk da cewa lamarin ba jiya ya faru ba, amma ya faru ne a makon jiya. Muna aiki tare da sauran hukumomin tsaro don ganin mun kuɓutar da mutanen da abin ya shafa."

- Akogun Adetunji Adeleye

Legit Hausa ta tuntuɓi jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan jihar, Misis Funmilayo Odunlami, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ta ce a tura saƙon waya ne domin ta ba ta jin abin da ake cewa sosai.

"Tura min saƙo ne ta waya bana jin abin da kake cewa sosai."

- Misis Funmilayo Odunlami

Sai dai, ba ta dawo da amsar saƙon ba bayan an tura mata.

Ƴan bindiga sun kashe malamin addini

Kara karanta wannan

An shiga fargaba da ƴan bindiga suka yi garkuwa da ɗan Majalisa a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka wani malamin addini a jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.

Ƴan bindigan sun kashe Rabaran Tobias Chukwujekwu Okonkwo a garin Ihiala a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng