"An Samu Tsaro a 2024," Gwamnan a Arewa Ya Yabawa Shugaban Kasa Tinubu
- Gwamna Caleb Mutfwang ya ce lamarin tsaro a jihar Filato ya inganta a shekarar 2024 idan aka kwatanta da abubuwan da suka faru a bara
- Mutfwang ya ce a bana sun yi shagalin kirismeti cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali saɓanin bara da ta zo da zubar da jini
- Ya kuma tabbatarwa al'ummar jihar Filato cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na Filato, a ranar Juma'a ya bayyana cewa tsaro ya inganta sosai a jihar a shekarar 2024.
Mutfwang ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar da ya kai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Legas.
Gwamnan ya bayyana cewa ba a samu wani mummunan tashin hankali a Filato lokacin kirismetin 2024 ba kamar yadda aka sha fama a baya, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya damu da rikicin Filato
Caleb Mutfwang ya ce:
"Na zo nan na gana da shugaban ƙasa wanda ya damu matuka da matsalar tsaron jihar Filato, idan baku manta ba bara a irin wannan lokacin Filato na cikin jimami.
"Shugaban ƙasa ya damu da tsaron mu, kuma yanzu ga shi kowa yana gani mun yi bikin kirismeti cikin kwanciyar hankali, muna tunkari sabuwar shekara."
Tsaro ya inganta a Filato a 2024
Gwamnan ya kara da cewa a wannan shekarar al’amuran tsaro sun inganta sosai a Filato idan aka kwatanta da bara, sakamakon kokarin da jami’an tsaro suke yi.
"Koda yaushe jami'an tsaro na nan a shirye kuma suna iya bakin ƙoƙarinsu, mun zuba dukiya a fannin fasaha tare da haɗa kan al'ummarmu," in ji shi.
Gwamnan ya yabawa shugaba Tinubu bisa matakan da yake ɗauka na samar da tsaro, tare da tabbatat da cewa za su mara masa baya, rahoton This Day.
Gwamnan Filato ya shirya tunkarar miyagu
Duk da har yanzu ana kai hare-hare mara daɗi, Gwamna Muftwang ya ce idan aka duba gaba ɗaya lamarin tsaro ya inganta fiye da bara.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin kakkabe dukkan nau'ikan miyagun laifuka a faɗin jihar.
Ƴan sanda sun samu nasarori a Filato
A wani labarin, kun ji cewa yayin da 2024 ke bankwana, rundunar yan sandan Filato ta bayyana nasarorin da dakarunta suka samu a shekara guda.
Rundunar ta ce ƴan sanda sun cafke mutanen da ake zargi da aikata laifuka kala daban-daban 859 tare da ƙwato makamai daga hannun miyagu.
Asali: Legit.ng