Bayan Zargin Shugaban Nijar, Sarakuna Sun Fadi Gaskiya kan Zargin a Yankunansu

Bayan Zargin Shugaban Nijar, Sarakuna Sun Fadi Gaskiya kan Zargin a Yankunansu

  • Sarakunan gargajiya da mazauna kan iyaka a Sokoto da Kebbi sun musanta zargin shugaba Abdourahamane Tchiani cewa Najeriya ta ajiye sojojin Faransa
  • Mazauna Balle, Marake, da Kurdula sun tabbatar da babu sansanin sojojin kasashen waje a yankunansu, sun bukaci Tchiani ya guji zarge-zargen karya
  • Dagacin gundumar Balle, Alhaji Aminu Aliyu ya karyata zarge-zargen Tchiani inda ya ce babu gaskiya a maganarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sarakunan gargajiya da mazauna kan iyaka a Sokoto da Kebbi sun karyata zargin shugaba Abdourahamane Tchiani na Nijar cewa akwai sojojin Faransa a Najeriya.

Mazauna yankunan har ila yau, sun ce babu wasu alamu na ba sojojin ketare mafaka a yankunansu kamar yadda ake zargi.

Wasu mazuna iyakar Sokoto da Nijar sun karyata zuwan sojojin Faransa
Wasu sarakunan gargajiya a Sokoto da Kebbi sun musanta cea akwai sojojin Faransa a iyakokinsu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Tchiani: Sarakuna sun musanta zargin Shugaban Nijar

Vanguard ta ruwaito cewa wasu mazauna kauyuka a Sokoto da Kebbi sun tabbatar da babu wata shaida ta sansanin horar da sojoji a yankunan.

Kara karanta wannan

Bayan zargin Najeriya, shugaba Tchiani na shan suka daga yan Nijar, sun ba shi shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dagacin Balle, a karamar hukumar Gudu, Alhaji Aminu Aliyu ya ce zargin shugaba Tchiani ba shi da tushe kuma babu rahoton sansanin sojojin Faransa.

Wani shugaban al'umma, Malam Abdurahman Usman ya ce mazauna Marake, Kurdula sun tabbatar da babu wani sansani, kuma suna da kyakkyawar alaka da ’yan Nijar.

Mazauna iyakoki sun musanta zargin akwai sojojin Faransa

Malam Kabiru Muhammad, wani mazaunin Ruwa-Wuri, ya ce akwai matsalar ’yan ta’addan Lakurawa, amma babu sansanin sojojin kasashen waje a yankinsu, cewar Leadership.

Sarkin Arewan Araba, Alhaji Abubakar Yusufu, ya musanta zargin sansanin sojoji kuma ya ce sojojin Nijar na kai farmaki a yankunansu da dare.

Alhaji Muhammad-Kaka, dagacin gundumar Bayawa a Kebbi, ya ce zargin Tchiani na iya kawo rikici, yana mai yabawa da kokarin sojojin Najeriya.

Sojoji Faransa: Yan Nijar sun soki Shugaba Tchiani

Mun ba ku labarin cewa Shugaban Nijar, Abdourahmane Tchiani, na shan suka daga ‘yan ƙasarsa kan zargin da ya yi wa Najeriya.

Kara karanta wannan

'Siyasa ce': An zargi Nijar da neman hada gaba mai tsanani tsakanin yan Arewa da Tinubu

Tchiani ya yi ikirarin cewa Najeriya ta bai wa sojojin Faransa mafaka kusa da Tafkin Chadi tare da kafa sansanonin horar da ‘yan ta’adda.

'Yan Nijar sun ce zargin Tchiani ba shi da hujja, suna danganta hakan da gazawarsa bayan wata 17 da ya kifar da Bazoum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.