'Yan Sanda Sun ba 'Yan Najeriya Mafita kan Ayyukan Gurbatattun Jami'ai
- Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ja kunnenta jami'anta masu yin amfani da sunan Sufeto-Janar wajen aikata rashin gaskiya
- Kakakin rundunar a cikin wata sanarwa ya jaddada cewa ko kaɗan ba su goyon bayan wannan halin rashin ɗa'ar na gurɓatattun jami'an
- Muyiwa Adejobi ya shawarci ƴan Najeriya da suka riƙa kai rahotanni ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi magana kan yadda wasu gurɓattun jami'anta ke amfani sunan IGP Kayode Egbetokun, wajen aikata ba daidai ba.
Rundunar ƴan sandan ta jaddada matsayinta na adawa da amfani da suna ko ofishin Kayode Egbetokun, da wasu ɓata garin jami'ai ke yi wajen aikata ɓarna.
Ƴan sanda sun koka kan gurɓatattun jami'ai
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, ya sanya a shafin X ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muyiwa Adejobi ya nuna damuwarsa kan yadda waɗannan jami’an suke gudanar da ayyukansu, wanda ya ce hakan na ɓata sunan rundunar.
Adejobi ya ce manufar amfani da sunan IGP ɗin ita ce tsoratar da mutane kan cewa yana sane da ayyukan waɗannan gurɓatattun jami'an kuma ya amince da haramtattun ayyukansu.
Ƴan sanda sun ba ƴan Najeriya mafita
Kakakin ƴan sandan ya buƙaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu na rashin ɗa’a ko zamba da jami’an ƴan sanda ke yi ga hukumomin da suka dace.
Ya buƙaci a kai rahotannin ga shugabannin sassan da ke amsar koke-koke a jihohinsu ko kuma kwamishinan ƴan sanda.
"Rundunar ƴan sandan Najeriya ta damu da yadda wasu jami'ai ke ci gaba da nuna rashin ɗa’a, wanda ke zubar da ƙima da mutuncinta."
"Duk da gargaɗi da matakin ladabtarwa da ake ɗauka kan waɗanda aka fallasa, har yanzu wasu jami’an na ci gaba da aikata wannan abin kunyan."
"Wani abin damuwar shi ne yadda ake amfani da suna da ofishin Sufeto-Janar na ƴan sanda wajen aikata waɗannan haramtattun ayyukan."
- Muyiwa Adejobi
Ƴan sanda sun cafke masu laifi a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta cafke mutum 859 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban a shekarar 2024.
Ƴan sandan sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa daga hannun masu aikata laifuffuka tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng