Sojoji Sun Cafke Dan Boko Haram da Jami'in Tsaro Mai Taimakon 'Yan Ta'adda

Sojoji Sun Cafke Dan Boko Haram da Jami'in Tsaro Mai Taimakon 'Yan Ta'adda

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar cafke wani ɗan ta'addan Boko Haram a jihar Taraba da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Sojojin sun yi nasarar cafke ɗan ta'addan ne bayan sun samu sahihan bayanan sirri kan miyagun ayyukan da yake aikatawa
  • Jami'an tsaron sun kuma cafke wani jami'in tsaro wanda yake haɗa baki da masu garkuwa da mutane

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), sun cafke wani ɗan ta'addan Boko Haram a jihar Taraba.

Dakarun sojojin sun yi nasarar cafke ɗan ta'addan ne a yankin Garba Chede da ke ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Sojoji sun cafke dan Boko Haram a Taraba
Sojoji sun kama dan ta'addan Boko Haram a jihar Taraba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ɗan ta'addan Boko Haram ya shiga hannu

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bajinta, sun cafke masu laifi 859 a jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargin mai suna Nura Yakubu, an kama shi ne bayan an samu sahihan bayanan sirri a kansa.

Bincike ya nuna cewa Nura Yakubu wanda yake sayar da abinci yana da hannu wajen ba da mafaka ga ƴan ta'addan Boko Haram da aka tura jihar Taraba domin ayyukan ta'addanci.

Kyaftin Olubodunde Oni ya ce sakamakon binciken da aka gudanar ya alaƙanta shi da ƴan ƙungiyarsa da yin garkuwa da wani ɗan kasuwa mai suna Arinze da ɗan Alhaji Ibrahim, kwanakin baya a ƙauyen Garbatau da ke ƙaramar hukumar Bali.

Sojoji sun cafke jami'in tsaro

Hakazalika biyo bayan sace wani Hakimi a ƙaramar hukumar Jalingo da aka yi a ranar 27 ga Nuwamba, 2024, da sakinsa bayan biyan kuɗin fansa, sojoji sun ƙara ƙaimi wajen gano wadanda suka aikata laifin.

Wannan ƙoƙarin ya kai ga cafke Musa Suito a ranar 18 ga watan Disamba, 2024, a cikin babban birnin Jalingo.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina, sun sheke tsageru masu yawa

Wanda ake zargin ɗan ƙungiyar ƴan banga ne da ke samar da tsaro ga fitattun mutane da masu hannu da shuni, inda ya yi amfani da matsayinsa wajen tattara bayanai domin masu garkuwa da mutane.

Kayayyakin da dakarun sojojin suka ƙwato daga gare shi sun haɗa da ƙaramar bindiga ƙirar gida guda ɗaya da harsashi guda biyu.

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun.sojoji sun yi raga-raga da sansanonin ƴan ta'adda a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.

Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa a farmakin da suka mai musu ta sama da ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng