"Allah Ya Ba Ku Haƙuri," Shugaban APC Ganduje Ya Aika Sako ga Gwamna Namadi
- Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yi ta'aziyya ga gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi bisa rasuwar mahaifiyarsa da ɗansa
- Ganduje ya yi addu'ar Allah ya sa su a gidan Aljannah Firdausi kuma ya ba gwamna da iyalansa hakurin jure wannan rashi
- Ya bukaci gaba ɗaya ƴan APC da su sanya mai girma gwamnan cikin addu'o'insu Allah ya ba shi ikon cin wannan jarabawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana alhininsa tare da jajantawa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi bisa rashe-rashen da ya yi.
Ganduje ya mika sakon ta'aziyya ga mai girma gwamnan Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa da kuma babban ɗansa.
Shugaban APC ya miƙa sakon ta'aziyya
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran ofishin shugaban APC na ƙasa, Edwin Olofu ya fitar kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya bayyana rashe-rashen guda biyun a matsayin waɗanda ba za a iya maye gurbinsu ba, ba kawai ga dangin Namadi ba, har ma da jihar Jigawa baki daya.
Shugaban APC ya ce mahaifiya da ɗan Gwamna Namadi da Allah ya yi wa rasuwa ginshiƙai ne a iyalinsa saboda halayensu na kirki da yi wa al'umma hidima.
Ganduje ya yi addu'ar Allah ya jikansu
“A madadin APC da daukacin shugabannin jam’iyyar, ina mika sakon ta’aziyya ga Gwamna Umar Namadi, da iyalansa, da al’ummar Jigawa a wannan lokaci mai cike da kalubale.
“Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya sa waɗanda suka rasu su samu hutu na dindindin a cikin Al-Jannah Firdaus, ya kuma bai wa iyalansu ikon jure raɗaɗin rashin da ba zai misaltu ba,” in ji shi.
Ganduje ya kuma yi kira ga abokai, masu fatan alheri da ’yan APC a fadin kasar nan su sa yalan Namadi cikin addu’a tare da karfafa masu gwiwa a wannan lokaci na jarabawa.
Buhari ya tura sakon ta'aziyya ga Umar Namadi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi ta'aziyya ga Gwamna Umar Namadi kan rashin mahaifiya da ɗansa.
Buhari ya roki gwamnan ya rungumi kaddara, yana mai cewa mutuwar uwa da ɗa cikin sa'o'i 24 ba ƙaramar jarabawa bace.
Asali: Legit.ng