Yan Sanda Sun Gano Motar Ɗan Majalisar da Ƴan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Shi
- Dakarun ƴan sanda sun gano motar ɗan Majalisar dokokin jihar Anambra, Hon. Justice Azuka wanda ake fargabar an yi garkuwa da shi
- Mai magana da yawun ƴan sanda na jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya ce dakarun tsaro na ci gaba da kokarin ceto ɗan majalisar
- A ranar Talata da daddare ne aka nemi ɗan majalisar aka rasa a hanyarsa ta komawa gida domin shagulgulan kirismeti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Rundunar ‘yan sanda a Anambra ta gano motar ɗan Majalidar dokokin jihar, Hon Justice Azuka wanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi.
Kakakin ‘yan sanda a jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Yan bindiga sun sace ɗan Majalisar Anambra
Premium Times ta rahoto cewa an yi garkuwa da Mista Azuka ne a daren ranar Talata a kan titin Ugwunapampa da ke karamar hukumar Onitsha ta Arewa a Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Onitsha ta Arewa a majalisar dokokin jihar, na hanyar komawa gida domin bikin Kirsimeti lokacin da aka yi garkuwa da shi.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Anambara, SP Ikenga ya ce dakarun caji ofis na Inland Town ne suka yi nasarar gano motar ɗan Majalisar.
Ƴan sanda sun gano motar ɗan Majalisar
Ya ce gano motar ya biyo bayan matakan da dakarun ƴan sanda suka ɗauka da nufin ceto Hon Azuka cikin ƙoshin lafiya, rahoton Punch.
SP Ikenga ya ce jami’an ‘yan sandan sun hangi motar ne a gefen titin Upper Iweka, mai tazarar kilomita da dama daga wurin da harin ya faru.
Sai dai bai bayyana samfurin motar ba, amma hoton da aka makala a sanarwar ya nuna cewa motar da aka gano kirar Ford SUV ce.
"Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, Nnaghe Obono, ya buƙaci ‘yan sandan da aka tura su kara kaimi wajen ceto dan majalisar da aka sace," inji Mista Ikenga.
Ƴan bindiga sum kashe malamin coci
A wani rahoton, an ji cewa ƴan bindiga sun hallaka wani limamin coci, Rabaran Tobias Chukwujekwu Okonkwo a jihar Anambra.
An ruwaito cewa maharan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne a yankin ƙaramar hukumar Ihiala ranar Alhamis da ta gabata.
Asali: Legit.ng