"Za Ku Gane Shayi Ruwa Ne," Gwamna Ya Fusata da Yan Bindiga Suka Kashe Mutum 11
- Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya ɗauki zafi kan harin da aka kashe mutane 11 a kauyen Anwase a ƙaramar hukumar Kwande
- Alia ya bayyana cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa masu hannu a mummunan harin sun fukanci fushin doka
- Gwamnan ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan da suka rasa ƴan uwansu tare da fatan samun lafiya ga waɗanda suka jikkata a harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia ya lashi takobin hukunta maharan da suka kashe mutum 11 a kauyen Anwase a karamar hukumar Kwande ta jihar Benuwai.
Gwamnan ya ce duk wanda ke da hannu a mummunan harin wanda aka kashe bayin Allah da ba su ji ba kuma ba su gani ba zai ɗanɗana kuɗarsa.
Alia ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Benuwai, Tersoo Kula ya fitar ranar Juma'a, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Alia ya yi Allah-wadai da harin
Gwamnan ya yi Allah-wadai da harin, wanda rahotanni suka ce an kashe mutane 11, ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi adalci ga wadanda abin ya shafa.
Hyacinth Alia ya ce ba ya jin daɗin harin da ake kaiwa mutanen jihar duk da kokarin da gwamnatinsa take yi na tabbatar da zaman lafiya.
Ya bukaci hukumomin tsaro su kara zage dantse wajen sanya ido kan motsin ƴan ta'adda tare da tabbatar da tsaro a kauyuka da birane.
Gwamna ya lashi takobin hukunta mahara
Alia ya ce:
"Ina mai tabbatar muku cewa wadanda suka aikata wannan aika-aika za su girbi abin da suka shuka.
"A tunaninsu ba a san su ba, amma su sani ba za a bari su ci gaba da aikata wannan ɗanyen aiki ba."
Gwamna Alia ya miƙa sakon ta'aziyya
Gwamnan ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin tare da jajantawa wadanda suka jikkata.
Ya kuma ɗaukar masu alkawarin cewa zai yi duk mai yiwuwa ya tabbatar da duk mai hannu a harin ya fuskanci fushin doka.
Ƴan bindiga sun kashe lauya a Benue
Kun ji cewa ƴan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun hallaka wani matashin lauya a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya.
Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce tuni dakarunta suka fara gudanar da bincike da nufin kamo maharan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng