Sakon Buhari ga Gwamna Namadi bayan Rashin da Ya Yi, Ya Fadi Abin da Ya Kamata Ya Yi
- Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ta'azziyar rasuwar mahaifiyar Gwamna Umar Namadi da dansa
- Buhari ya ce mutuwar dattijuwar da dansa al’amari ne da Allah ya kaddara wanda babu yadda aka iya
- Tsohon shugaban kasar ya ce mutuwar mahaifiya da ɗa a rana guda abu ne mai ciwo, amma dole a rungumi ƙaddara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajantawa Gwamna Umar Namadi kan rashin da ya yi.
Buhari ya yi kira ga gwamnan ya rungumi mutuwar mahaifiyarsa da ɗansa a matsayin ƙaddara daga Allah.
Buhari ya tura sakon ta'azziya ga Gwamna Namadi
Buhari ya bayyana ta'aziyyarsa cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya bayyana cewa wannan mutuwa ta mahaifiya da ɗa a rana ɗaya abu ne mai ciwo wanda ba za a taba mantawa da shi ba.
"Ko da yake wannan abin takaici ne, Allah ne ya tsara haka, kuma dole ne mu amince da ƙaddarar Ubangiji mai hikima."
"Duk wanda ya san abin da ke cikin zuciya zai ji tausayin wannan jarabawa, amma ya kamata ka ɗauki wannan don ƙarfafa imaninka ga Allah."
- Muhammadu Buhari
Buhari ya ba Gwamna Umar Namadi shawara
Buhari ya yi kira ga gwamna Namadi ya yi amfani da wannan lokaci a matsayin jarabawa don ƙara kusantar Allah da kuma sadaukar da rayuwarsa ga al’amuran jama’a.
Buhari ya isar da ta'aziyyarsa ga dangin gwamnan, abokan arziki, da al’ummar jihar Jigawa baki ɗaya.
Daga bisani, Buhari ya yi addu'ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu, ya kuma ba waɗanda su ke raye ƙarfin zuciya don jure wannan babban rashi.
Abba Kabir ya jajanta wa gwamna Namadi
Kun ji cewa an sake shiga jimami a jihar Jigawa bayan rasuwar yaron Gwamna Ahmed Umar Namadi kwana ɗaya bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Gwamna Namadi kan rasuwar Abdulwahab Umar Namadi.
Matashin ya rasu ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2025 sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng