Nadin Sarki Ya Zama Rigima da Aka ba Tsohon Mataimakin Gwamna Sarauta

Nadin Sarki Ya Zama Rigima da Aka ba Tsohon Mataimakin Gwamna Sarauta

  • Jami'an tsaro sun mamaye fadar Ilesa da ke jihar Osun yayin da aka naɗa sabon basarake a yankin
  • Tsohon mataimakin gwamnan Osun, Clement Adesuyi Haastrup ya samu sarautar Owa-Obokun na Ijesa
  • Clement Haastrup ya doke 'yan takara tara a zaben sarauta da aka gudanar a gundumar Ilesa ta Yamma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - A yau Juma'a 27 ga watan Disambar 2024 jami'an tsaro suka mamaye Ilesa yayin da aka naɗa sabon sarki a jihar Osun.

Yayin nadin sarautar, an zabi Clement Adesuyi Haastrup, tsohon mataimakin gwamnan Osun, a matsayin Owa-Obokun na Ijesa.

Ana zaman dar-dar bayan nada sabon Sarki a Osun
Masu nadin sarauta sun zabi tsohon mataimakin gwamnan a matsayin Owa-Obokun na Ijesa a jihar Osun. Hoto: Legit.
Asali: Original

An nada sabon Sarkin Owa-Obokun na Ijesa

The Nation ta ce haka ya biyo bayan rasuwar Oba Gabriel Aromolaran a watan Satumbar 2024, wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 42.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ɓatan malami, yan bindiga sun bindige malamin addini, an bukaci addu'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan rasuwarsa, manyan sarakunan gargajiya sun ayyana lokacin makoki tare da fara tantance sabon sarki.

A wata sanarwa da Isaac Haastrup, kakakin gidan sarauta na Bilaro Olu-Odo, ya tabbatar da cewa Clement Adesuyi Haastrup ne aka zaba a matsayin Owa-Obokun Ajimoko III.

"Ya doke 'yan takara tara a zabe na gaskiya da aka gudanar a ofishin gundumar Ilesa ta Yamma kusa da hanyar Ilesa-Oshogbo."
"Masu zaben sun hada da mutane kamar Obaala, Chif Ibitoye da Ogboni Ipole da Oba Omokehinde Oyeleye."

- Cewar sanarwar

Yadda tsohon mataimakin gwamna ya samu sarauta

Bayan nadin sarautar, shugabar gundumar Ilesa ta Yamma, Mrs Felicia Olabimtan, ta bayyana cewa Looja Clement Adesuyi ne ya samu rinjaye.

Olabimtan ta ce daga cikin masu zabe, shida ne suka kada kuri’a, yayin da wasu bakwai ba su cancanci kada kuri’a ba.

A halin yanzu, jami’an tsaro sun karade birnin Ilesa, inda aka ga sojoji da sauran jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

An sake yin babban rashi a Najeriya, tsohon kwamishina ya riga mu gidan gaskiya

Minista ya shiga takarar neman sarauta

Kun ji cewa bayan mutuwar marigayi Oba Gabriel Adekunle Aromolaran, tsohon Minista a Najeriya ya shiga jerin masu neman sarauta a jihar Osun.

Farfesa Stephen Debo Adeyemi ya nuna kwadayinsa kan kujerar inda ya ce yana da kwarewa sosai a rayuwarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.