An Sake Yin Babban Rashi a Najeriya, Tsohon Kwamishina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Sake Yin Babban Rashi a Najeriya, Tsohon Kwamishina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon kwamishinan yaɗa labarai a jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91 a duniya
  • Kungiyar ƴan jarida (NUJ) reshen jihar Kwara ta tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ta fitar ta hannun sakatare ranar Alhamis
  • Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin tare da addu'ar Allah ya sa shi a gidan Al-Jannah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Allah ya yi wa tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya, Alhaji Abdulrahim Adisa rasuwa.

Abdulrahim Adisa ya riga mu gidan gaskiya ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, 2024 yana da shekaru 91 a duniya.

Alhaji Ibrahim Adisa.
Tsohon kwamishinan yada labarai a Kwara ya rasu yana da shekaru 91 Hoto: Yunus Olalekan
Asali: Facebook

Sakataren ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) reshen Kwara, Olayinka Alaya ne ya tabbatar da rasuwar tsohon kwamishinan a wata sanarwa, Tribune Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi shirinsu bayan iftila'in harin bam a Sokoto, ya ba da gudunmawar kudi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wa tsohon kwamishina jana'iza

Alaya ya ce an gudanar da Sallar Janazar marigayi ɗan jaridar da misalin karfe 10:00 na safe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya kuma ƙara da cewa bayan an sallace shi, an birne gawarsa a makabartar musulmi da ke garin Osere a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Marigayi Alhaji Abdulrahim Adisa ya rike mukamin Babban Manaja na gidan jaridar Herald mallakar gwamnatin jihar Kwara a lokacin rayuwarsa.

Haka nan kuma ya riƙe muƙamin kwamishinan yada labarai da sadarwa da kuma shugaban karamar hukumar Moro.

Gwamnan Kwara ya mika sakon ta'aziyya

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya yi ta'aziyya a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar.

Abdulrazaq ya tuna da irin gudunmawar da marigayin ya bayar a harkar yada labarai, musamman a matsayinsa na tsohon ma’aikacin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Gwamna Abdulrazaq ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga ɗaukacin ‘yan jarida, musamman ma’aikatan jaridar Herald da kuma iyalan Alhaji Abdulrahim Adisa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ɓatan malami, yan bindiga sun bindige malamin addini, an bukaci addu'o'i

Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya sa Al-Jannah Firdaus ta zama makomarsa, ya kuma ba iyalansa haƙuri.

Tsohon AIG ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Emmanuel Adebola Longe ya kwanta dama.

Kungiyar lauyoyi ta jihar Oyo ta tabbatar da rasuwar tsohon AIG, inda ta mika sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikin marigayin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262