Gwamna Bala Mohammed Ya Sauya Sakataren Gwamnati, An Nada Sabon SSG
- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya nada sabon Sakataren gwamnati tare babban sakatarensa bisa wasu dalilai
- Tsohon Sakataren gwamnatin jihar, Barista Kashim Ibrahim ya ajiye aiki ba tare da an bayyana dalilan hakan ba
- A wannan rana ne za a ranstar da sabbabin wadanda aka nada mukaman biyu, inda aka bayya gogewarsu a kan aiki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi - Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya maye gurbin Barista Kashim Ibrahim da Aminu Hammayo a matsayin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG).
Haka kuma, ya maye gurbin tsohon Babban Sakatare ga gwamna, Samaila Burga, wanda ya yi murabus domin zama Shugaban Jam’iyyar PDP a jihar.

Source: Facebook
The Guardian ta ce a sanarwar da Mukhtar Gidado, mai magana da yawun gwamnan, ranar Juma’a an ce Hashimu Kumbala ne ya maye gurbin Burga, yayin da Hammayo ya zama sabon SSG.
Dalilin sauya SSG a jihar Bauchi
Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Barista Kashim Ibrahim ya yi murabus daga mukamin Sakataren Gwamnatin Jiha ba tare da an bayyana dalilin ba.
Mukhtar Gidado ya bayyana cewa;
"Hammayo gogaggen ma’aikaci ne wanda ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa a matsayin jami’in gwamnati, ya yi suna wajen kwarewa, aiki tukuru, da sadaukarwa wajen hidimar al’umma."
Za a rantsar da masu mukaman Bauchi
Aminu Hammayo, wanda ya taba zama SSG a baya, kafin wannan sabon nadin nasa, shi ne kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi na jihar Bauchi.
Gwamnati ta bayyana cewa:
“A matsayinsa na SSG, zai bayar da mahimmin goyon baya na gudanarwa da shawara ga gwamna, tare da tabbatar da daidaito a tsakanin hukumomin gwamnati."
Dukkannin sababbin masu mukaman, Aminu Hammayo da Hashimu Kumbala za su sha rantsuwar fara aiki a yau.
Gwamnan Bauchi ya aika sako ga Tinubu
A baya kun ji cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya tunatar da gwamnatin Najeriya, karkashin mulkin Bola Ahmed Tinubu irin wahalar da jama'a ke ciki na kunci.
Sai dai ya shaida wa mazauna jihar Bauchi cewa ya na aiki tukuru da taimakon mukarrabansa wajen kawo sauki ga halin da ake ciki na matsi da kuncin rayuwa da ake ji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

