Gwamna Aliyu Ya Yi Bayani kan Batun Jefa Bama Baman da Sojoji Suka Yi a Sakkwato
- Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu ya yi alhini bisa rasuwar mutum 10 sakamakon kuskuren sojoji a kauyukan Gidan Bisa da Runtuwa
- Ahmed Aliyu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tuntuɓi shugabannin sojoji domin gudanar da bincike da kare aukuwar haka nan gaba
- Ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu tare da tabbatar masu cewa gwamnatinsa za ta taimaka masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu ya nuna takaicinsa kan jefa bama-baman da sojoji suka yi kan fararen hula a yankin karamar hukumar Silame ta jihar Sakkwato.
Akalla mutane 10 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon farmakin da sojoji suka kai ta sama kan ƴan ta'addan Lakurawa ranar Kirismeti.

Source: Facebook
Gwamna Aliyu ya tuntuɓi shugabannin sojoji
Ahmed Aliyu ya ce ya tuntuɓi hukumomin soji domin tabbatar da an gudanar da bincike kan lamarin wanda ya jawo rasa rayukan bayin Allah, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan
NAF: Rundunar sojin sama ta yi magana kan rahoton kuskuren kashe bayin Allah a Sokoto
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar kan lamarin, gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don tallafa wa iyalan wadanda abin ya shafa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Sakkwato za ta zauna da hukumomin soji domin tabbatar da an ɗauki matakan kare aukuwar irin hakan nan gaba.
Harin sojoji: Gwamnatin Sakkwato ta yi ta'aziyya
"Ba mu ji daɗin abin da ya faru a kauyukan Gidan Bisa da Runtuwa da ke ƙaramar hukumar Silame ba. Wannan al'amari ya faru ne sakamakon kuskuren harin sojoji.
"Mutanen da ba su ji ba basu ga ni ba sun rasa rayukansu wasu kuma sun ji rauni. A matsayin gwamna, na yi matuƙar takaicin wannan rasa rayuka da za a iya kaucewa."
"A madadin gwamnati da jama'ar Sokoto, ina mika ta'aziyyata ga iyalan da suka rasa 'yan uwansu. Muna kuma addu'ar Allah ya ba wadanda suka jikkata lafiya."
- Ahmed Aliyu.
Gwamnan ya ƙara da cewa tuni ya tuntuɓi hukumomin soji kan lamarin, inda ya yi kira al'ummar Sakkwato su ci gaba da addu'ar samun zaman lafiya a kasar nan.
Hukumar sojin sama ta fara bincike
A wani rahoton, an ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta nanata cewa ƴan ta'adda suka kai wa hari a Sakkwato ba fararen hula ba.
Rundunar ta ce duk da haka za ta gudanar da bincike kan rahoton da ake yaɗawa cewa faramakin saman ys taɓa wasu fararen hula a ƙauyuka biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
