"Tinubu Na Neman Tayar da Fitina," Gwamna Ya Dura Kan Shugaban Ƙasa
- Gwamnan Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP ya buƙaci Bola Tinubu ya canza tunani kan kudirin gyara haraji
- Bala Mohammed ya ce idan Tinubu ya dage sai ya aiwatar da kudirin, to ya sani yana gayyato rikici ne da kansa
- Ya ce kudirin ba ƙaramar illa ba ce ga Arewacin Najeriya domin wasu gwamnonin ba za su iya biyan ma'aikata albashi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya janye kudirinsa na sauya fasalin haraji.
Ƙauran Bauchi ya gargaɗi shugaban ƙasar da cewa idan ya kafe dole sai ya canza dokar haraji, hakan ka iya tayar da fitina da rikici a ƙasar nan.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a wurin bikin kirismeti da aka shirya a Bauchi ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, 2024, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu na neman gayyato rikici a Najeriya
Kalaman Kauran Bauchi, shugaban gwamnonin PDP na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan Shugaba Tinubu ya ce ba gudu ba ja da baya a batun sauya fasalin harji.
A wata tattainawa da ƴan jarida, shugaban ƙasar ya ce ba dole kowa ya amince da kudirin ba, amma dai yana nan kan bakarsa.
Da yake martani kan lamarin, Gwaman Bauchi ya ce idan har kudirin harajin ya zama dola, wasu jihohin ba za su iya biyan ma'aikata albashi ba.
A cewar Bala Mohammed, babu ta inda kudirin dokar ya yi wa Arewa gata face illa wacce ka iya jawo gwamnoni su gaza suake haƙƙin da ke kansu, Vanguard ta kawo.
"Kudirin haraji ba alheri ba ne" - Bala
"Dangane da kudirin haraji, ba tsari ba ne mai kyau ga Arewa domin ba za su samu kudin da za mu biya ku albashi ba.
"Ya zama dole su saurare mu, idan ba haka ba to suna shirin gayyato rikici wanda ba abu ne mai kyau ba. Mu muka zaɓi shugaban kasa a nan jihar da sauran jihohi."
"Dole su saurare mu, ba zai yiwu su kinkimo tsarin da zai fifita jiha guda kaɗai ba. Wannan ba batu ba ne na addini ko ƙabila, magana ce ta haɗin kai da mulkin ƙasa."
- Sanata Bala Mohammed.
Gwamna Bala ya kara ba al'umma haƙuri
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya kara bai wa al'umma haƙiri bisa wahala da tsadar rayuwar da suke fuskanta.
Gwamnan ya ce babu daɗi a ce mutanen da suka zabe shi su na wahala, inda ya bada tabbacin yin bakin kokarinsa wajen kawo sauƙi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng