'Ba Mulkin Soja Ake ba,' Gwamna Ya yi Kalamai Masu Zafi ga Tinubu kan Kudirin Haraji
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nuna damuwarsa kan yadda shugaba Bola Tinubu ke nacewa kan kudirin haraji
- Gwamna Bala ya bayyana cewa kudirin harajin zai cutar da yankin Arewa tare da ƙarfafa wani yanki na Najeriya
- Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake nazarin manufofinta na tattalin arziki domin rage wahalar da jama’a ke fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kalubalanci kudirin gyaran haraji na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ba su dace da halin da ake ciki ba.
Yayin da yake jawabi ga mabiya addinin Kirista a Bauchi, ya yi gargadin cewa irin waɗannan manufofin na iya jefa Najeriya cikin ƙarin matsalolin tattalin arziki.
Legit ta gano jawabin da gwamna Bala Mohammed ya yi ne a cikin wani sako da hadiminsa, Lawal Mu'azu Bauchi ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan jihar Bauchi ya soki kudirin haraji
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa kudirin haraji ya fi karkata ga wani yankin Najeriya, wanda hakan ya nuna ba zai amfani Arewacin kasar ba.
Bala Mohammed ya ce kudirin ba zai taimaka wa Arewa ba, kuma ba za su iya samun kuɗin biyan albashi ko gina hanyoyi ba idan aka aiwatar da shi.
Ya yi kira ga shugabannin ƙasa su yi taka-tsan-tsan da manufofin da za su kawo wa jama'a wahala, yana mai cewa rashin sauraron jama'a zai jawo tarzoma.
'Ba mulkin soja ake a Najeriya ba,' Gwamna Bala
A cikin jawabin nasa, Bala Mohammed ya ce ya zama wajibi shugabanni su saurari jama’a tare da yin abubuwan da za su kawo sauƙi a rayuwarsu.
Vanguard ta wallafa cewa gwamnan ya ce ba mulkin soja ake yi ba da za a tilastawa mutane manufofin da za su kuntatawa rayuwarsu.
Bala Muhammad ya ce idan aka ga manufofi ba za su amafani jama’a ba, ya kamata gwamnati ta saurari mutane, yana mai cewa shugabanci na gari shi ne wanda ke jin ra’ayoyin jama’a.
Ana gina makarantar Dahiru Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi ya kaddamar ginin takafariyar makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa makarantar za ta zamo ta zamani kuma za a gina irinta a dukkan kananan hukumomin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng