Ministan Tinubu Ya Tona Yadda Samawa 'Yan Jiharsa Ayyukan Tarayya Masu Yawa
- Ministan yada labaran Najeriya, Mohammed Idris, ya bayyana cewa ya samar da guraben aiki na tarayya guda 30 ga ‘yan asalin jihar Neja
- Ministan ya ce ya yi wasu manyan ayyuka a garinsa Malagi, ciki har da gina makarantar Islamiyya, masallatai, da aikin wutar lantarki.
- Mohammed Idris ya jaddadawa al'umma cewa manufofin shugaba Bola Ahmed Tinubu za su samar da ci gaba mai dorewa ga Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Ministan Yada Labarai da Wayar da kan Al'umma, Mohammed Idris, ya bayyana yadda ya ke taimakon 'yan jihar Neja.
Mohammed Idris ya tabbatar da cewa ya samar da guraben aikin gwamnatin tarayya da dama ga ‘yan asalin jihar Neja tun bayan nadinsa a matsayin minista.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa Mohammed Idris ya lissafo ayyukan da ya aiwatar a garinsa na Malagi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake maida martani kan korafin wani basarake a mazabarsa wanda ya zarge shi da gazawa wajen samar da guraben aiki ga mutanensa.
Minista ya samar da aiki ga 'yan jiharsa
Mohammed Idris ya ce ya yi hanyar nadin Jibrin Baba Ndace a matsayin Darakta Janar na VON, tare da wasu guraben aiki 30 na tarayya.
“Tun lokacin da aka nada ni minista, na tabbatar da nadin Jibrin Baba Ndace a matsayin Darakta Janar na VON.
"Haka kuma, na samar da guraben aiki guda 30 ga ‘yan asalin jihar Neja.”
- Mohammed Idris
Minista ya kaddamar da ayyuka a mahaifarsa
Jaridar Tribune ta wallafa cewa Mohammed Idris ya yi bayanin ne yayin kaddamar da wasu ayyuka a garinsa na Malagi, cikin karamar hukumar Gbako a jihar Neja.
Ayyukan sun hada da gina sababbin masallatai, samar da wutar lantarki, ruwan sha, da gyaran makarantar firamare a yankin.
Ya ce ayyukan sun kasance ne domin inganta rayuwar al’umma tare da karfafa ilimin addini wanda zai tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.
Minista ya ba 'yan Najeriya hakuri
A wani rahoton, kun ji cewa minstan yada labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri.
Mohammed Idris ya bayyana cewa nan gaba kadan za a fara gani a kasa kan tsare tsaren da Bola Tinubu ya kawo tun hawansa mulki a 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng