Jihohin Najeriya Sun Yi Kasafin Sama da Naira Tiriliyan 74 don Magance Talauci a 2025

Jihohin Najeriya Sun Yi Kasafin Sama da Naira Tiriliyan 74 don Magance Talauci a 2025

  • Jihohin Kudu maso Yamma ne su ke a kan gaba wajen ware kasafin kudin 2025 mafi tsoka a tsakanin takwarorinsu
  • Zuwa yanzu, jihohi 35 da gwamnatin tarayya sun gabatar da kasafin kudinsu a gaban majalisu don ba su damar aiki
  • Jihar Ribas da rigingimun siyasa ya dabaibayeta da babban birnin tarayya Abuja har yanzu ba su kai ga gabatar da na su ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Domin rage talauci da inganta rayuwar jama’a a shekarar 2025, Gwamnatin Tarayya da jihohi 35 daga cikin jihohi 36 na ƙasar sun tsara kashe Naira tiriliyan 74.249 a matsayin kasafin kudin 2025.

Jihar Rivers, wadda ke cikin rikicin siyasa, da Babban Birnin Tarayya, Abuja, ba su bayyana kasafin kudinsu ba tukuna.

Kara karanta wannan

Babban malami a Arewa ya dura kan gwamnati, ya ce ita ta jawo rasa rayuka a jihohi 3

Tinubu
Gwamnatoci 2 ne ba su gabatar da kasafin 2025 ba har yanzu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kidddigar Jaridar Vanguard ta ce Naira tiriliyan 74.249 da aka gabatar na iya ƙaruwa nan da ƙarshen 2025, domin har yanzu majalisun dokoki ba su amince da yawancin kasafin kudin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jihohi za su kashe kasafin 2025

Kididdigar kasafin kudin jihohi daban-daban, ya nuna cewa an tsara kashe Naira tiriliyan 35.676, wato 48.05% a kan ayyukan raya ƙasa.

An gano cewa jihohin Kudu maso Yamma ya zo na farko da Naira tiriliyan 6.202, yayin da Arewa maso Gabas ke ƙarshen da Naira tiriliyan 2.610 na yawan kasafin 2025.

Jihohin da suka fi yawan kasafin kuɗi

Daga cikin jihohi, waɗanda suka fi yawan kasafin kuɗi sun haɗa da:

• Legas (Naira tiriliyan 3.005)

• Neja (Naira tiriliyan 1.5)

Ogun (Naira tiriliyan 1.0545)

• Delta (Naira biliyan 979.2)

• Enugu (Naira biliyan 971.8)

• Akwa Ibom (Naira biliyan 955)

Jihohin da suka yi ƙarancin kasafin kuɗi

Waɗanda suka fi ƙarancin kasafin kuɗi sun haɗa da:

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware N27bn domin rabawa Buhari, Jonathan da mataimakansu a 2025

• Gombe (Naira biliyan 320.11)

Yobe (Naira biliyan 320.811)

• Ekiti (Naira biliyan 375.79)

• Nasarawa (Naira biliyan 382.57)

• Ebonyi (Naira biliyan 396.59)

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin 2025

A baya mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin shekarar 2025 a gaban majalisar dokoki, ya ce za a kashe N549b don inganta rayuwar jama'a.

Bayan gabatar da kasafin ne shugaban majalisar, Jibril Isma'il Falgore ya tabbatar wa da gwamnan cewa za su nazarci kasafin, tare da amincewa da shi a cikin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.