Garambawul: Gwamna a Arewa Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 7 da Hadimai 8

Garambawul: Gwamna a Arewa Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 7 da Hadimai 8

  • Gwamna Ahmed Aliyu ya nada sababbin kwamishinoni, manyan sakatarori da masu ba da shawara domin inganta aikin gwamnati
  • Mai girma Gwamnan jihar na Sokoto ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashin gaskiya a tsakanin ma'aikatansa
  • Sababbin kwamishinonin da aka nada sun hada da Farfesa Isa Muhammad Maishanu, Farfesa Attahiru Ahmed Sifawa sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya rantsar da sababbin kwamishinoni bakwai, manyan sakatarori tara, da kuma masu ba da shawara takwas.

An yi nadin ne domin cike gurbin wadanda suka yi murabus don zama shugabannin kananan hukumomi, tare da karfafa aiki da cigaban majalisar zartarwa.

Gwamnan Sokoto ya yi garambawul a majalisar zartarwar jiharsa
Gwamnan Sokoto ya nada sababbin kwamishinoni, hadimai da sakatarorin dindindin. Hoto: @honnaseerbazzah
Asali: Facebook

A wurin bikin nadin, Gwamna Ahmed Aliyu ya jaddada muhimmancin amfani da kwarewar su wajen yi wa al'umma aiki da gaskiya, a cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yadda aminin Turji ke tsula tsiyarsa, wasu a yankin Sokoto sun roki gwamnati alfarma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Sokoto ya yi sababbin nade-nade

Ya sake nanata manufofin gwamnatinsa na rashin yarda da cin hanci, yana jan hankalin wadanda aka nada da su zama jakadun gudanar da aiki cikin gaskiya.

Gwamnan ya cee:

“Gwamnatina za ta tabbatar kowa ya amfana da albarkatun jiharmu cikin adalci, tare da mayar da hankali kan cigaba da shugabanci nagari.”

Ya kara da cewa:

"Nadin wadannan kwararru zai inganta aikin gwamnati da kuma karfafa tattaunawa tsakanin gwamnati da jama'a, domin samun amana da goyon bayan al’umma."

Sunayen wadanda gwamna ya nada

Babban mataimaki na musamman a kan sababbin kafafan sadarwa da soshiyal midiya ga gwamnan jihar Sokoto, Hon. Naseer Bazza ya wallafa sunayen a shafinsa na X.

Kwamishinoni:

1. Abba Muhammad Mualledi

2. Farfesa Isa Muhammad Maishanu

3. Farfesa Attahiru Ahmed Sifawa

4. Dakta Faruku Umar Abubakar

5. Dakta Abubakar Mohammed Zayyana

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: Gwamna ya gayyato 'yan China domin koyar da noman zamani

6. Injiniya Mustapha Mohammed

Masu ba da shawara na musamman:

1. Almu Tsoho Kwandawa

2. Abubakar Ahmed Sokoto

3. Dakta Isa Mua’zu

4. Dakta Muhammad Bello Marnona

5. Umar Ahmadu

6. Dakta Muhammad Umar Yabo

7. Salisu Lawali Gandi

Manyan Sakatarori:

1. Ado Ibrahim Sabon Birni

2. Muhammad Abubakar Umar Yabo

3. Mustapha Abubakar Alkali

4. Ibrahim Muhammad K

5. Habibu Isa

6. Bello Sodangi

7. Bashar Muhammad Maigari

8. Lawali Sada

9. Muhammad Bello Yusuf

Gwamna Ahmed Aliyu ya kai ziyarar ta'aziyya

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ziyarci garuruwan da ake zargin jiragen sojojin saman Najeriya sun sakar masu bama bamai.

A yayin da aka ce mutane akalla 10 ne suka mutu a harin, an ce Gwamna Aliyu ya gana da al'ummar garuruwan biyu domin jajanta masu da kuma kwantar da hankalinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.