Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Katsina, Sun Sheke Tsageru Masu Yawa
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi ruwan wuta kan miyagun ƴan ta'adda a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
- Jami'an tsaron sun lalata sansanonin ƴan ta'addan a kusa da tsaunin Birchi da ke ƙaramar hukumar Danmusa ta.jihar Katsina
- Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda masu tare da raunata wasu shugabanninsu guda biyu a yayin farmakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun lalata sansanonin ƴan ta'adda da dama a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun lalata sansanonin ƴan ta’addan ne a kusa da tsaunin Birchi da ke ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun fatattaki ƴan ta'adda
Sojojin na ƙasa tare da hadin gwiwar sojojin sama sun kashe ƴan ta’adda da dama tare da raunata wasu manyan shugabanninsu masu suna Manore da Dogo Nahalle a farmakin, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya ce an gudanar da farmakin ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ta’addanci a yankin, waɗanda suka haɗa da kai hare-hare a ƙananan hukumomin Danmusa, Safana, da Kankara na jihar a ranar 19 ga watan Disamba 2024.
Ya ce dakarun sojojin da suka haɗa da na ƙasa da sama sun kai farmaki kan sansanonin a ƙoƙarinsu na wargaza ayyukan ƴan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan.
Daraktan ya bayyana cewa majiyoyi sun bayyana cewa hare-haren sun yi sanadiyyar hallaka ƴan ta’adda masu yawa ciki har da raunata wasu fitattun shugabanninsu Manore da Dogo Nahalle.
Dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun ƴan ta'adda da suka addabi mutane a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Dakarun sojojin sun tura ƴan ta'adda guda 181 a cikin mako guda tare da ceto mutane 50 da miyagun suka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng