Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ziyarci Buhari, an Gano Abin da Suka Tattauna
- Tsohon shugaban majalisar dattawa ya kai ziyara ga Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina
- Sanata Ahmad Lawan ya ziyarci tsohon shugaban ƙasan na Najeriya ne a ranar Laraba, 25 ga watan Disamban 2024
- Tsohon shugaban majalisar dattawan da Muhammadu Buhari sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi ƙasar nan da siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Sanata Ahmad Lawan ya ziyarci Muhammadu Buhari ne a gidansa dake Daura a jihar Katsina.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba sanatan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ezrel Tabiowo ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan mai wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa ya isa gidan tsohon shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe 12:40 na rana a ranar Laraba kuma ya samu tarba mai kyau, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Buhari ya tattauna da Sanata Ahmad Lawan
Ezrel Tabiowo, ya ce tsohon shugaban majalisar dattawan da tsohon shugaban ƙasar sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi ƙasar nan da siyasa.
Tabiowo ya ƙara da cewa, Sanata Ahmad Lawan ya miƙa saƙon fatan alheri na al'ummar mazaɓarsa da iyalansa ga tsohon shugaban ƙasar da iyalansa.
"Sanata Lawan ya godewa tsohon shugaban na Najeriya bisa jagorancin da ya yi a zamaninsa tsakanin watan Mayun 2015 zuwa Mayu 2023 da kuma ci gaba da jajircewarsa ga ci gaban Najeriya."
"Ya kuma nuna jin daɗinsa ga Shugaba Buhari bisa irin tarbar da aka yi masa da kuma yadda yake ci gaba da ba shi shawarwari."
"A martanin da ya mayar, tsohon shugaban kasar ya nuna jin daɗinsa ga Sanata Lawan kan ziyarar da kuma ci gaba da goyon bayan da yake ba shi."
- Ezrel Tabiowo
Dalilin Buhari na ƙin cire tallafin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana dalilin da ya sanya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi cire tallafin man fetur a lokacin mulkinsa.
Tsohon hadimin Buhari, Femi Adesina ya bayyana cewa Buhari ƙi cire tallafin fetur ne saboda baya son sanya talakawa cikin wani hali
Asali: Legit.ng