'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ana Tsaka da Bikin Kirsimeti, Sun Hallaka Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ana Tsaka da Bikin Kirsimeti, Sun Hallaka Bayin Allah

  • Ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Benue yayin da mutane suke cikin halin bikin Kirsimeti a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutane 12 yayain da suka yi garkuwa da wasu ƙananan yara bakwai yayin harin
  • Wata majiya ta bayyana cewa babba daga cikin yaran da aka sace shi ne mai shekara shida da haihuwa a duniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a jihar Benue ana tsaka da bikin Kirsimeti.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyukan Yaav da Mbakyol na ƙaramar hukumar Kwande, inda suka kashe sama da mutane 12 tare da sace yara bakwai.

'Yan bindiga sun kai hari a Benue
'Yan bindiga sun hallaka mutum 12 a Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta ce wani mazaunin ƙauyen Mbadura da ya samu mafaka a Jato-Aka, Lawrence Akeregba, ya tabbatar mata da aukuwar lamarin ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

"Babu tausayi": Kusa a PDP ya caccaki Tinubu, ya fadi halin da ya jefa 'yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Benue

Ya bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da ƙananan yara bakwai, inda babbansu shi ne mai shekara shida, yayin da ƙaraminsu ke da shekara biyu.

"Maharan sun mamaye ƙauyukan Yaav da Mbakyol na yankin Turan ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma lokacin da mafi yawan mutane suke gida tare da iyalansu."
"Sun kashe mutane 12, sun jikkata wasu da dama, sannan suka yi awon gaba da ƙananan yara yayin da aka nemi wasu mutanen aka rasa."
"Matasanmu suna duba dazuzzukan da ke kusa saboda har yanzu akwai mutanen da ba a gani ba da suka haɗa da mata da yara."
"An kwaso gawarwaki tara daga wajen da suka kai harin yayin da aka gano wasu uku a cikin daji. Akwai yiwuwar za a iya gano wasu gawarwakin."

- Lawrence Akerigba

Lawrence Akerigba ya bayyana sunayen waɗanda aka kashen da suka haɗa da Vanen Iorvihi, Mike Azege, Anyisa Akpa, Ausa Imbior, orwua Abur Hwande, Iornumbe Tse, Zaki Ashivor Mbailuve Tyohemba, Terhemba Tyohemba Jim Ierkwagh da Ijeyol Ierkwagh.

Kara karanta wannan

Ana shirin Kirsimeti, yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, ASP Catherine Anene domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai, kakakin ƴan sandan ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan harin domin ba ta samu wani rahoto a kai ba.

"Ban samu wannan rahoton ba. Ba ni da masaniya a kan lamarin."

- ASP Catherine Anene

Ƴan bindiga sun sace matafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun tare matafiya a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Ƴan bindigan waɗanda ake zargin suna da alaƙa da Bello Turji sun tilastawa dukkanin mutanen da ke cikin motar tafiya zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng