An Rufe Babbar Kasuwa a Kano kan Zargin Karuwanci, Malamin Musulunci Ya Koka

An Rufe Babbar Kasuwa a Kano kan Zargin Karuwanci, Malamin Musulunci Ya Koka

  • Karamar Hukumar Garun Malam ta rufe Kasuwar Tumatur ta Kwanar Gafan saboda zargin ayyukan fasadi, karuwanci da wasu munanan dabi'u
  • Shugaban karamar hukumar, Hon. Aminu Salisu Kadawa, ya tabbatar da rufe kasuwar tare da umartar masu kasuwa su fice kafin 1 ga Janairu, 2025.
  • Malamin addini, Imam Abdullahi Yusif Chiromawa, ya bayyana damuwarsa kan illar ayyukan fasadi ga tarbiyyar yara a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumomi a Karamar Hukumar Garun Malam ta jihar Kano sun rufe Kasuwar Tumatur ta Kwanar Gafan.

An rufe kasuwar saboda zargin ayyukan fasadi da suka hada da karuwanci, zina, luwadi da sauran munanan dabi'u.

Gwamnatin Kano ta rufe wata kasuwa kan fasadi
Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata kasuwa kan zargin ayyukan fasadi. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

An rufe kasuwar Kano kan ayyukan fasadi

Shugaban karamar hukumar, Hon. Aminu Salisu Kadawa, shi ya tabbatar wa Daily Trust yana mai cewa an dauki matakin ne don dawo da tsari a yankin.

Kara karanta wannan

Bayan kama yan uwansa, Turji ya ba gwamnati umarni, ya fadi abin da zai faru a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kadawa ya ce duk yan kasuwa dole ne su fice daga kasuwar kafin 1 ga Janairu, 2025, inda ya yi gargadi kan saba umarni.

“Yayin duba yadda kasuwar ta zama cibiyar karuwanci da sauran munanan dabi'u da suka saba da manufar kasuwar, dole ne a rufe ta don dawo da tsari.”
“Wannan wuri ya zama mafakar 'yan daba, masu fashi da makami, karuwai da sauran masu laifi."

- Hon. Aminu Kadawa

Malamin Musulunci ya nuna damuwa kan lamarin

Shugaban karamar hukumar ya tabbatar da cewa za a sanar da ranar bude kasuwar bayan sake duba ayyukanta, cewar Tribune.

Malamin addini, Imam Abdullahi Yusif Chiromawa, ya nuna damuwa kan illar ayyukan fasadi a tarbiyyar yara a yankin.

“Kasuwar ta zama cibiyar zina, luwadi da karuwanci ga matasa har ma da matan aure."

- Imam Chiromawa

Gwamnan Kogi ya rufe kasuwa kan ta'addanci

A baya, kun ji cewa Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo ya ba da umarnin rufe kasuwar Zango saboda taɓarɓarewar tsaro a yankin Osara.

Kwamishinan yaɗa labarai a jihar, Kingsley Fanwo ya ce gwamna ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano ana ɓoye ƴan ta'adda a kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.