Dangote Ya Fadi Lakanin dake Ruguzo da Farashin Man Fetur a Najeriya, Ya Jero Dalilai
- Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa yanayin kasuwa ne ya sa farashin mai ya fara sauka
- Bayanin nasa na zuwa bayan matatarsa ta rage farashin man fetur zuwa N935 bayan kulla yarjejeniya da gidan man MRS
- Wannan ta sa kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bi sahu wajen rage farashin man fetur dinsa a gidajen man da ya mallaka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana dalilin da ya sa aka fara samun saukin litar man fetur a fadin kasar nan.
Dangote ya ce dalilin rage farashin man fetur zuwa N899.50 kan kowace lita a matatarsa ya faru ne saboda yadda kasuwar mai ta sauya a Najeriya a halin yanzu.

Asali: Getty Images
Dangote ya yi wannan karin haske ne yayin wata tattaunawa da aka nuna a wani shirin talabijin na Arise TV da aka wallafa a YouTube a kan sauye-sauyen da ake samu yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote zai kare muradin matatarsa
A cewarsa, babban nauyinsa shi ne kare muradun kamfaninsa mai darajar biliyoyin daloli tare da tabbatar da dorewar jarin da aka yi.
Ya ce;
“Rage farashin ya yi daidai da abin da yanayin kasuwa ya tsara, bari in fadi hakan kawai, wata matatar mai ce da muka zuba jari fiye da dala biliyan 20, kuma ina ganin dole ne mu kare muradunmu da jarinmu.”
An fara samun saukin farashin man fetur
A ranar 19 ga Disamba, 2024, matatar mai ta Dangote ta rage farashin man fetur daga N970 zuwa N899.50 kan kowace lita ga ‘yan kasuwa.
Wannan ya sa NNPCL ya saukar da farashinsa zuwa N899 kan kowace lita, inda daga baya kuma matatar ta Dangote ta sanar da hadin gwiwarta da MRS don rage farashin mai.

Kara karanta wannan
'Ku koyi rayuwa a haka': Tinubu ya ba yan Najeriya satar amsa kan tsadar wutar lantarki
IPMAN da Dangote sun shiga yarjejeniya
A wani labarin, kun ji yadda kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta kulla yarjejeniya da matatar Dangote domin tabbatar da samun saukin farashin litar mai.
Shugaban kungiyar IPMAN ta kasa, Maigandi Garima ya tabbatar da cewa za su fara sayar da fetur a kan sabon farashin N935 bayan cimma matsaya da matatar Dangote.
Asali: Legit.ng