NAF: Rundunar Sojin Sama Ta Yi Magana Kan Rahoton Kuskuren Kashe Bayin Allah a Sokoto
- Rundunar sojin sama watau NAF ta jaddada cewa ƴan ta'addar Lakurawa jirgin yaƙi ya kaiwa farmaki a jihar Sakkwato
- Amma duk da haka rundunar ta ce za ta gudanar da bincike kan rahotanni da ke cewa jirgin ya yi kuskuren sakin bam kan wasu fararen hula
- A ranar Laraba ne aka samu labarin mutuwar mutum 10 sakamakon kuskuren jirgin yaƙin sojojin da ya farmaki ƴan ta'adda a kauyuka biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta ce za ta fara gudanar da bincike kan yadda jirgin yaƙi ya yi ruwan bama-bamai a wasu kauyuka biyu a Sakkwato ranar Laraba.
A cewar mazauna yankin, lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa da ke karamar hukumar Silame.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kuskuren jefa bama-baman ya yi ajalin fararen hula 10 yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda jirgi ya saki bama-bamai a Sakkwato
Mazauna yankin sun ce jirgin sojojin ya kawo farmaki ne kan 'yan ta'addar Lakurawa, garin haka ne ya jefa bama-bamai kan wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Sai dai a wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar sojin Operation Fansar Yamma, Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce Lakurawa suka kai wa hari.
A cewarsa, sai da suka tabbatar da wuraren na da alaƙa da ƴan ta'addan Lakurawa kafin su kaddamar da hare-hare ta sama.
Rundunar sojin sama ta yi magana
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya dage cewa an kai harin ne bisa ingantattun bayanai sirri daga majiyoyi da dama.
Ya ce sai da rundunar ta tabbatar da wuraren na da alaƙa da ƴan Lakurawa sannan ta tura jirgin ya yi masu luguden wuta.
Sai dai ya ba da tabbacin cewa za a gudanar da cikakken bincike kan rahotannin da aka samu na kashe fararen hula.
“An kai harin ne bisa sahihan bayanan sirri daga majiyoyi da dama, tare da tabbatar da ingancin bayanan ta hanyar sa ido ta sama.
"Amma duk da haka, za mu gudanar da bincike kan yiwuwar taɓa fararen hula yayin farmakin, za mu sanar da al'umma duk abin da aka gano," in ji Akinboyewa.
Gwamna Aliyu ya kai ziyara kauyukan 2
A wani rahoton mun kawo maku cewa Gwamna Ahmed Aliyu na Sakkwato ya kai ziyara kauyukan da sojoji suka kashe fararen hula 10 bisa kuskure.
Gwamnan wanda da shi aka yi wa mamatan sallah, ya ba da tallafin Naira miliyam 20 ga iyalan waɗanda ibtila'in ya shafa.
Asali: Legit.ng