Matar Tsohon Gwamna Ta Soki Gwamnan APC kan Bikin Tunawa da Marigayi Mijinta

Matar Tsohon Gwamna Ta Soki Gwamnan APC kan Bikin Tunawa da Marigayi Mijinta

  • Uwargidan tsohon gwamnan Ondo, Betty Akeredolu, ta yi kaca-kaca da gwamnatin jihar kan shirin gudanar da taron tunawa da mijinta
  • Betty Akeredolu ta ce ita da danginta ba su san da batun taron ba, tana bayyana shi a matsayin taron damfara
  • Hakan ya biyo bayan mutuwar marigayi Rotimi Akeredolu a watan Disambar 2023 bayan fama da jinya a Jamus

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Uwargidan tsohon gwamnan Ondo, Betty Anyanwu-Akeredolu ta soki gwamnatin jihar Ondo kan shirin gudanar da bikin tunawa da mijinta.

Uwargidan marigayin ta kuma caccaki da gwamna Lucky Aiyedatiwa kan shirin gudanar da taron tunawa marigayi Rotimi Akeredolu ba tare da saninsu ba.

Matar marigayi tsohon gwamnan ta caccaki gwamntin jihar Ondo
Matar marigayi tsohon gwamnan ta zargi shirya damfara kan bikin tunawa da mijinta, Rotimi Akeredolu. Hoto: @adaowere1.
Asali: Twitter

Gwamnatin Ondo ta shirya karrama marigayi, Akeredolu

Betty ta bayyana haka ne a yau Alhamis 26 ga watan Disambar 2024 a shafin X inda ta ce ko kadan ba a mutunta marigayin.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Tinubu ta gaza," Jigon APC ya amince sun ba ƴan Najeriya kunya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar Ondo ta shirya taron ne don tunawa da ayyukan marigayi Akeredolu, musamman rawar da ya taka.

Kakakin gwamna Aiyedatiwa, Ebenezer Adeniyan, ya ce za a ci gaba da shirya taron duk da kalaman uwargidan tsohon gwamnan.

"Da fatan za ku kasance tare da mu ranar Jumma’a yayin da muke girmama tsohon gwamnanmu."

- Ebenezer Adeniyan

Uwargidan marigayin ta ce ita da iyalinta ba su da masaniya kan wannan taro kuma ta bayyana taron a matsayin wani shiri na 'yaudara da damfara'.

A cikin rubutunta, Betty ta zargi gwamna da kokarin amfani da taron don samun kudi da sunan marigayin.

"Lucky ba ya nufin gaskiya, Wane mutunta ayyukan Akeredolu? Taron banza ne, ni da iyalina ba mu san da wannan ba, wannan shiri ne na karya."
"Ba za ku iya tsare abubuwan da Aketi ya yi ba, Wannan ya wuce gona da iri, Lucky, kana kokarin bata sunan Aketi, amma ba za ka yi nasara ba."

Kara karanta wannan

Yunwa: PDP ta alakanta turmutsitsin da ya hallaka jama'a da manufofin Tinubu

- Betty Akeredolu

An caccaki matar marigayi tsohon gwamna

Kun ji cewa matar marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta jawo kanta zagi da kuma mijinta da ke cikin kabari.

Ana zargin Betty Akeredolu ta yi rubutu a shafin X inda ta kira Najeriya da gidan 'zoo' da bai yi wa yan kasar dadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.