Gombe: Motar Shinkafa Ta Kwace, Direba Ya Mitsitstsike Masu Tattakin Kirsimeti
- Wasu bayin Allah sun gamu da mummunan hadari a lokacin da su ke tattakin bikin Kirsimeti a jihar Gombe
- An ruwaito cewa wata motar shinkafa ce ta kwace daga hannun direba, inda ta kutsa cikin ayarin Kiristocin da ke tattaki
- Mutanen na kan hanyarsu ta kai ziyarar da gaisuwar Kirsimeti zuwa fadar Sarkin Gombe da gidan gwamnatin jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe - Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta bayyana cewa mutane 22 sun ji raunuka yayin da wata mota ta kutsa cikin jerin ayarin masu bikin Kirsimeti.
Cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Gombe, Buhari Abdullahi, ya ce hatsarin ya faru da misalin karfe 2 na rana.
A sakon da kakakin ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce wata mota kirar Volkswagen Sharon mai dauke da buhunan shinkafa ta kwace daga hanya inda ta kutsa cikin Kiristocin a Tumfure da ke Gombe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shiga fargaba bayan hadarin Kirsimeti a Gombe
Rundunar ‘yan sandan Gombe ta ce wasu Kiristoci da ke hanyarsu ta kai gaisuwa fadar Sarkin Gombe da gidan gwamnati sun gamu da iftila’i.
Mai magana da yawun rundunar, Buhari Abdullahi ya ce direban motar, wanda ba a san ko waye ba har yanzu ya tsere daga wurin, yayin da wasu matasa suka kona motar.
Gombe: Mutane sun jikkata a hadarin Kirsimeti
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta bayyana cewa ba a samu asarar rai a mummunan hadarin da ya afku ba, amma mutane 22 sun ji raunuka iri-iri.
Tuni aka kai wadanda suka ji rauni zuwa Cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FTH) da asibitin kwararru na Gombe domin samun kulawa, yayin da aka shiga farautar direban.
Rundunar ta ce tawagar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da shugabannin kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) na aiki tare don tabbatar da zaman lafiya da doka.
'Yan bindiga sun kwace abincin Kirsimeti
A baya, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun wafce abinci da sauran kayan ciye-ciye da wani bawan Allah ya sayo domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti.
Lamarin ya faru ne a kauyen Gidan Abe da ke Kachia a jihar Kaduna, inda aka samu rahoton cewa 'yan bindigar ba su illata kowa ba.
Asali: Legit.ng