An Shiga Fargaba da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Ɗan Majalisa a Najeriya
- An shiga tashin hankali da wasu ƴan bindiga suka sace ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Justice Azuka a Onitsha
- Wani makusancinsa ya ce har yanzu babu wani labari game da inda ɗan majalisar yake tun bayan sace shi a ranar Talata
- Rundunar ƴan sanda reshen jihar Anambra ta ce tuni dakarunta suka bazama domin ceto shi da kamo waɗanda suka sace ɗan majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Wasu mahara sun yi garkuwa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Onitsha ta Arewa a majalisar dokokin jihar Anambra, Justice Azuka.
An tattaro cewa an yi garkuwa da Azuka ne a ranar Talata da daddare yayin da yake komawa gida a kan titin Ugwunapampa a Onitsha.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Azuka, jigon jam'iyyar LP ya ɗare kan kujerar ɗan majalisa ne bayan kotu ta tsige Douglas Egbuna na PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga sun sace ɗan majalisar Anambra
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigar sun tasa keyarsa zuwa cikin daji bayan tare shi a kan titi.
Wani na kusa da shi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa tun bayan sace dan majalisar, har yanzu ba a san inda yake ba.
Ya ƙara da cewa a iya saninsa maharan da suka yi garkuwa da shi ba su tuntuɓi kowa da nufin neman kuɗin fansa ba.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan lamarin, amma mazauna yankin sun nuna kaduwa da sace ɗan majalisa sukutum.
Ƴan sanda sun bazama neman maharan
Sannan sun yi kira da a dauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro da ta yi katutu a yankinsu da wasu sassan jihar Anambra.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra a ranar Laraba, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana kokarin kubutar da dan majalisar.
A rahoton The Nation, Ikenga ya ce:
"Yan sanda sun bazama da nufin ceto ɗan majalisar dokokin Anambra mai wakiltar Onitcha, Hon Justice Azuka tare da kama waɗanda suka sace shi."
Yan bindiga sun sace fasinjoji a Ekiti
A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akalla 18 a hanyar zuwa Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun fara tuntubar iyalan matafiyan, sun nemi a biya N30m a matsayin fansar kowane mutum ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng