Jirgin Yaki Ya Saki Boma Bomai a Kauyukan Sokoto Yana Kokarin Kashe Lakurawa

Jirgin Yaki Ya Saki Boma Bomai a Kauyukan Sokoto Yana Kokarin Kashe Lakurawa

  • Wasu jiragen yaki da ke kokarin kashe Lakurawa sun kai hari kan kauyuka biyu a karamar hukumar Silame a Sokoto.
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama suka jikkata a harin
  • Shugaban karamar hukumar Silame ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai bayyana cewa ana ci gaba da bincike

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu suka samu munanan raunuka sakamakon wani hari da jirgin yaki ya kai a karamar hukumar Silame ta Jihar Sokoto.

Lamarin, wanda ya faru a safiyar Laraba da misalin karfe 7:00, ya shafi kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa.

Jirgin yaki
Jirgin yaki ya kashe mutane bisa kuskure a Sokoto. Hoto: Giang Huy
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wani mazaunin yankin Silame, Malam Yahya, ya ce kauyukan biyu suna kusa da dajin Surame, wanda ake danganta shi da zama mafakar Lakurawa da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Babban malami a Arewa ya dura kan gwamnati, ya ce ita ta jawo rasa rayuka a jihohi 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin yakin sojoji ya aukawa fararen hula

Tribune ta wallafa cewa jirgin yaki da aka tura domin kai farmaki kan Lakurawa ya yi kuskuren auka wa fararen hula a kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa.

Wani ganau ya shaida cewa sama da mutum 10 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren.

Hukuma ta tabbatar da harin jirgi a Sokoto

Shugaban karamar hukumar Silame, Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa suna ci gaba da tantance girman barnar da aka yi.

Abubakar Muhammad Daftarana ya kara da cewa mutanen kauyen suna zaune cikin kwanciyar hankali sai bom ya fara sauka a kansu.

'Yan sanda sun kaurace wa yin tsokaci

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i, ya ki yin tsokaci kan harin, yana mai cewa ba aikin ‘yan sanda ba ne.

Kara karanta wannan

An yi kare jini biri jini tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga

Tuni al’umma ke kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace domin kauce wa sake aukuwar irin wannan kuskuren.

'Yan sanda sun fafata da 'yan ta'adda a Imo

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda a jihar Imo ta sanar da mutuwar jami'anta guda biyu bayan fafatawa da 'yan ta'adda.

Legit ta wallafa cewa jami'an tsaro sun yi kare jini biri jini da 'yan ta'addar ne inda suka kashe uku a cikinsu suka kama wasu da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng