Rashin Tsaro: PDP Ta Jefi Tinubu da Kalubalen Tafiya daga Abuja zuwa Legas

Rashin Tsaro: PDP Ta Jefi Tinubu da Kalubalen Tafiya daga Abuja zuwa Legas

  • PDP ta zargi Shugaban Kasa Bola Tinubu da amfani da kididdiga na karya wajen fitar da rahoton habakar tattalin arzikin Najeriya
  • Jam’iyyar ta ce tsare tsaren gwamnatin APC da Tinubu ke jagoranta sun kara jefa ‘yan Najeriya cikin tsananin wahalar rayuwa
  • PDP ta ta kalubalanci Tinubu da ya yi tafiya daga Abuja zuwa Legas da mota domin fahimtar halin da talakawa ke ciki kan tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta yi kaca-kaca da shugaba Bola Ahmed Tinubu kan maganganunsa a tattaunawar da ya yi da manema labarai.

PDP ta ce Bola Tinubu ya dogara da kididdiga marasa tushe wajen fadin cigaban da aka samu a bangaren tattalin arzikin Najeriya.

PDP|Tinubu
PDP ta soki Tinubu kan cewa tsaro ya inganta. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Tribune ta wallafa cewa kakakin PDP na Kasa, Debo Ologunagba ne ya fitar da sanarwar inda ya ce maganganun shugaba Tinubu sun yi hannun riga da halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

'Ku yi mani addu'a': Tinubu ya roki yan kasa bayan jawabinsa da ya fusata al'umma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta jefi Tinubu da kalubale kan tsaro

PDP ta soki Tinubu kan cewa ‘yan Najeriya na iya yin tafiya lafiya ta hanyoyi, tana mai cewa matsalar ‘yan fashi, garkuwa da mutane, da rashin kyawun tituna na ci gaba da addabar kasar.

Jam'iyyar ta kalubanci Tinubu da ya yi tafiya daga Abuja zuwa Legas domin ganin gaskiyar abubuwan da ke faruwa na rashin tsaro idan da gaske yake.

PDP ta ce cunkoson jama’a da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 80 a wasu jihohi alama ce ta karuwar talauci karkashin mulkin APC.

Jam'iyyar PDP ta caccaki cire tallafin fetur

Jam’iyyar PDP ta zargi Shugaba Tinubu da dagewa kan kan cire tallafin man fetur ba tare da tanadar matakan rage wahalar da talakawa ke ciki ba.

The Cable ta wallafa cewa PDP ta ce matakin ne ya haifar da tsadar rayuwa, durkusar da masana’antu, da jefa miliyoyin mutane cikin talauci.

Kara karanta wannan

"Aikinmu ya na kyau:" Tinubu ya fadi kokarin da gwamnatinsa tayi wa Arewacin Najeriya

An bukaci Tinubu ya binciki Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya binciki gwamnatin Muhammadu Buhari.

Shehu Sani ya ce binciken gwamnatin Buhari a kan tsaro abu ne mai muhimmanci wajen magance cin hanci da rashawa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng