Ana Neman Hada Rikici a APC bayan Bukatar Tinubu Ya Binciki Buhari
- Shehu Sani ya soki Bola Tinubu bisa matsayinsa na kin amincewa da binciken kudin tsaro da ka kashe a zamanin Muhammadu Buhari
- Kwamred Sani ya ce rashin binciken yana nuna alamar halin ko-in-kula da Tinubu ya yi a kan cin hanci da rashawa a bangaren tsaro
- Wani matashi dan APC ya bayyanawa Legit cewa ko da an binciki gwamnatin Buhari ba sa tsammanin za a samu baraka a jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsayinsa na rashin binciken kudin tsaro a gwamnatin Buhari.
Shehu Sani ya bayyana cewa wannan matsayi na Bola Tinubu yana karo da binciken da ake yi wa tsohon shugaban babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television ranar Talata, Shehu Sani ya ce rashin binciken tamkar yafe cin hanci ne ga wadanda suka wawushe kudin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhimmancin bincike kudin tsaro
Tsohon sanatan ya bayyana cewa yana da muhimmanci shugaban kasa ya dawo baya domin gano yadda aka yi amfani da kudin jama’a a mulkin Buhari.
“Mun ga yadda ake binciken badakalar babban bankin CBN, amma idan aka tambaye shi game da ma’aikatar tsaro, sai ya ce ba zai bincika ba, wanda hakan ya saba wa adalci,”
- Sanata Shehu Sani
Sanatan ya ce kamata ya yi shugaban kasar ya nemi hujjojin da ke nuna cin hanci da rashawa a ma'aikatar tsaro domin bincike ba kawar da kai ba.
Hadarin kin binciken kudin tsaro
Shehu Sani ya ce rashin bincike tamkar tabbatar da halatta rashawa ne da gwamnati ke maganar yaka a yau da kullum.
Ya ce yin biris da abubuwan da suka faru a baya tamkar danne gaskiya ne da kuma karfafa gwiwar wadanda suka aikata laifi.
Sanatan ya yi kira ga shugaban kasa da ya tabbatar da cewa duk wani abu da ya shafi rashin gaskiya a baya an dauki mataki a kansa domin karfafa gaskiya da adalci.
Legit ta tattauna da dan APC
Wani matashin dan jam'iyyar APC, Aminu Abubakar ya ce yana fata Bola Tinubu ya binciki harkar tsaro a lokacin Buhari.
Aminu ya bayyana cewa Buhari ya yi gaskiya saboda haka ba abin da zai faru da shi kuma ya kamata a hukunta duk jami'insa da aka samu da laifi.
Ya kara da cewa ana binciken gwamnan CBN da ya yi aiki a karkashin Buhari kuma hakan bai haifar da gibi a jam'iyyar ba, saboda haka ba su tunanin wata baraka saboda bincike.
APC ta hango nasarar Tinubu a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC a Arewa ta Tsakiya ta ce akwai alamun da suka nuna Bola Tinubu zai yi nasara a 2027.
Masu ruwa da tsakin APC a jihar Benue sun ce hadin kai da ake samu a jam'iyyar alama ce da ke nuna za a maimaita nasarar da aka samu a 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng