"Ba 'Yan Bindiga ba ne": Shugaban Hukuma Ya Fadi Abin da Yafi Hallaka 'Yan Najeriya

"Ba 'Yan Bindiga ba ne": Shugaban Hukuma Ya Fadi Abin da Yafi Hallaka 'Yan Najeriya

  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa reshen jihar Kano, ya nuna damuwa kan yawaitar haɗurran mota da ake samu a Najeriya
  • Umar Matazu ya bayyana cewa kisan da ƴan bindiga ke yi bai kai yawan asarar rayukan da haɗurran mota ke jawowa ba
  • Ya ɓuƙaci kafafen yaɗa labarai da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama'a kan muhimmancin kiyaye dokokin tuƙi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano, Umar Matazu, ya bayyana abin da ya fi ɗaukar rayukan ƴan Najeriya.

Kwamandan na FRSC ya bayyana cewa haɗurran ababen hawa a Najeriya sun fi jawo asarar rayuka fiye da ayyukan ta’addanci da ƴan bindiga.

Kwamandan FRSC ya koka kan hadurran mota
Kwamandan FRSC reshen Kano ya ce hadurran mota na jawo asarar rayuka Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Twitter

Umar Matazu ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga sababbin shugabannin ƙungiyar ƴan jarida reshen jihar Kano a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

"Akwai kura kurai": Shugaba Tinubu ya tabo batun bincikar hafsoshin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haɗurran mota na jawo asarar rayuka

Ya yi ƙarin haske kan yawan mace-macen da ake samu sakamakon haɗurran mota idan aka kwatanta da waɗanda ayyukan ta’addanci ko ƴan bindiga ke haddasawa.

Umar Matazu ya jaddada buƙatar kafafen yaɗa labarai su ƙara ƙaimi domin wayar da kan jama'a game da kiyaye dokokin tuƙi da tallata bin ƙa'idojin zirga-zirga.

"Yawan mace-macen da haɗurran ababen hawa ke haddasawa ya zarce na ta'addanci, ƴan fashi da sauran miyagun ayyuka."
"Ba kasafai ake samun harin da ya kashe mutane sama da 10 ba, amma a wani hatsarin mota, ba baƙon abu ba ne samun asarar rayukan sama da mutum 40."
"Daga watan Oktoba zuwa yau, yawan mace-macen da ake samu daga haɗurran kan tituna ya zarce na ƴan ta’adda ko ƴan bindiga"

- Umar Matazu

Ma'aikatan jami'a sun yi hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani hatsarin mƙta ya ritsa da motar da kw ɗauke da ma'aikatan jami'ar jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.

Mummunan hatsarin motan ya yi sanadiyyar rasuwar mutane uku har lahira yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng