Kungiyar Addinin Musulunci Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Fasa Kaddamar da Kotun Shari'a
- Kungiyar Musulmin jihar Oyo ta ɗage bikin kaddamar da kotun shari'ar Musulunci da ta shirya ranar 11 ga watan Janairu, 2025
- A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce addinin Musulunci ya yi umarni da zaman lafiya don haka ta ɗage buɗe kotun sai baba ta gani
- Batun kaddamar da kotun dai ya fuskanci kalubale da suka daga mutane, wasu sun yi zargin hakan shirin Musuluntar da yankin ne
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Kungiyar addinin Musuluncin nan da ke shirin buɗe kotun shari'a a jihar Oyo ta lashe amanta bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo baya.
Ƙungiyar ƙarƙashin majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya ta ɗage kaddamar da kotun shari'ar Musulunci har sai baba ta gani.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Khadimul Muslimeen na Oyo, Imam Daud Igi Ogun, a ranar Talata, Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fasa kaddamar da kotun Musulunci a Oyo
Ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda a zauna lafiya domin addinin Musulunci ya fi son zaman lafiya.
Sanarwar ta ce:
"A madadin al'ummar Musulmin jihar Oyo muna sanar da jama'a cewa an ɗage buɗe kotun shari'ar da muka shirya kaddamarwa ranar 11 ga watan Janairu, 2025 har sai baba ta gani saboda zaman lafiya."
Yadda batun kotun ya tayar da ƙura
Tun farko dai wani katin gayyata da ya yaɗu a soshiyal midiya ya nuna ƙungiyar ta gayyaci Musulmi daga dukkan sassan Najeriya zuwa wurin buɗe kotun shari'a.
Ƙungiyar ta tsara kaddamar da kotun ne ranar 11 ga watan Janairu, 2024 a cibiyar addinin Musulunci da ke titin makarantar Oba Adeyemi a Oyo.
Sai dai lamarin ya sha suka daga mutanen Kudu maso Yamma, waɗanda galibi yarbawa ne, sun nuna rashin gamsuwa da abin da suka kira yunƙurin Musuluntar da yankin.
Sakamakon suka da ka-ce-na-ce da ya biyo baya ne ƙungiyar ta sanar da janye shirinta na buɗe kotun shari'ar Musulunci saboda a zauna lafiya.
Matasan Yarbawa sun yu fatali da kafa kotun
A wani rahoton, kun ji cewa matasan Yarbawa sun yi watsi da shirin kafa kotunan shari'ar Musulunci a Kudu maso Yammacin Najeriya.
Sun bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen dakile duk wani yunkuri da ka iya haifar da rikici da rashin zaman lafiya a tsakaninsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng