Ana Shirin Kirsimeti, Yaran Bello Turji Sun Yi Ta'asa a Sokoto
- Wasu ƴan bindiga da ake zargin suna da alaƙa da Bello Turji sun yi garkuwa da matafiya a jihar Sokoto da ke yankin Arewa
- Ƴan bindigan waɗanda ke ta'addancinsu a gabashin Sabon Birni sun yi garkuwa da matafiyan a ranar Talata, 24 ga watan Disamba
- Tantiran dai sun tilastawa mutanen fitowa daga cikin motar da suke tafiya sannan suka tafi da su zuwa cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai da ake zargin suna da alaƙa da Bello Turji sun yi garkuwa da matafiya a jihar Sokoto.
Ƴan bindigan waɗanda ke aiki a gabashin Sabon Birni a jihar Sokoto, sun yi garkuwa da matafiya guda bakwai da sanyin safiyar ranar Talata, 24 ga watan Disamban 2024.
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaran Bello Turji sun sace matafiya
Ƴan bindigan dai sun yi garkuwa da mutane bakwai ne waɗanda suka haɗa da mata shida da direba ɗaya da sanyin safiyar Talata.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan waɗanda ake zargin na da alaƙa da tantirin shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, ne suka kai harin.
Ƴan bindigan dai sun tare motar kasuwancin ne a kusa da ƙauyen Chin Golf.
Sun tilastawa matafiyan fita daga cikin motar sannan suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.
Bello Turji dai da yaransa sun yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare a jihohin Sokoto da Zamfara inda suke cin karensu babu babbaka.
Bello Turji ya kafa sabon sansani
A wani labarin kuma, kun ji cewa hatsabibin 'dan bindiga, Bello Turji, ya kafa sabon sansanin da ya ke gudanar da ayyukan ta'addanci.
Jagoran ƴan bindigan ya kafa sabon sansanin ne a dajin Indaduwa wanda ke a kusa da ƙauyen Bula a yankin Gundumi.
Sabon sansanin na Bello Turji dai ya shahara wajen kai hare-hare ga mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng