Yadda 'Yan Sanda Suka Kama Miyagu 30,313 da Bindigogi 1,984 a 2024

Yadda 'Yan Sanda Suka Kama Miyagu 30,313 da Bindigogi 1,984 a 2024

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da rahoto kan manyan nasarorin da ta samu a kan 'yan ta'adda da miyagu a 2024
  • 'Yan sanda sun kama mutane 30,313 bisa zarge-zarge daban-daban tare da kwato bindigogi 1,984 da tarin harsashi a fadin kasar nan
  • Sufeto Janar ya yaba da kokarin jami'an 'yan sanda, yana mai alkawarin ci gaba da sauye-sauye masu muhimmanci a 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta samu gagarumar nasara wajen yaki da laifuffuka a shekarar 2024.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce an kama mutane 30,313 tare da kwato bindigogi 1,984 da harsashi 23,250 a 2024.

Kara karanta wannan

An cafke jigon NNPP kan zargin sukar gwamna Zulum, ana fargabar kai shi kotu

30,313
Yan sanda sun kama mutane 30,313 a 2024. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jawabin ya fito ne yayin taron tattaunawa da manyan jami’an 'yan sanda a Abuja kamar yadda rundunar ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da 'yan sanda suka ceto a 2024

A jawabin sa, Sufeto Janar Kayode Egbetokun ya yabawa jajircewar jami’an 'yan sanda wajen rage laifuka da karfafa dangantaka tsakanin jama’a da 'yan sanda.

Punch ta wallafa cewa IGP Kayode Egbetokun ya ce cikin shekarar nan an samu nasarar ceto mutane 1,581 daga hannun masu garkuwa da mutane a jihohi.

Shirin inganta tsaro a shekarar 2025

Sufeto Janar ya bayyana cewa rundunar za ta mayar da hankali wajen amfani da fasahar zamani da dabarun aiki domin tunkarar kalubalen tsaro na shekarar 2025.

Ya bukaci manyan jami’an su rungumi sababbin kayan aiki da tsare-tsaren zamani da za su kara inganta aikin tsaro da bincike.

Ya ce za a yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwan karshen shekara tare da tabbatar da tsaro ga kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Yadda hukumar EFCC ta yi farautar manyan 'yan siyasar Najeriya a shekarar 2024

Sojoji sun kai farmaki wajen tsafe tsafe

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta samu nasara kan wasu 'yan ta'addar kungiyar IPOB a jihar Anambra.

Legit ta ruwaito cewa rundunar sojin ta rutsa 'yan ta'addar ne a wani waje da suke tsafe-tsafe kuma sun hallaka da dama daga cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng