Gwamna Ya Yi Rabon Babura ga Ma'aikata, Ya Fadi Amfanin Hakan
- Gwamnatin jihar Kebbi ta gwangwaje ma'aikatan da ke aiki a gidan gwamnati da baburan da za su riƙa zuwa wurin aiki da su
- Aƙalla ma'aikata 50 ne aka ba baburan a rabon da ake yi rukuni-rukuni a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi
- Kwamishinan ayyuka na musamman, Zayyanu Umar-Aliero ya ce ana ba da baburan ne domin ƙarawa ma'aikatan ƙwarin gwiwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris, ta yi rabon babura ga ma'aikatan da ke aiki a gidan gwamnati.
Gwamnatin jihar Kebbi ta raba babura aƙalla guda 50 ga ma'aikatan gidan gwamnati domin sanya su zuwa wurin aiki ba tare da fashi ba.
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Zayyanu Umar-Aliero ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kebbi ta ba ma'aikata babura
Kwamishinan ya gabatar da makullan babura guda biyar ga mutanen suka ci gajiyar shirin a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Zayyanu Umar-Aliero ya kuma bayyana cewa ana raba baburan ne a rukuni-rukuni.
"Mun raba babura ga wasu ma’aikatanmu da ke aiki a nan gidan gwamnati. Wannan yunƙurin an yi shi ne domin tabbatar da cewa suna zuwa aiki a kan lokaci.”
"Mun raba biyar a yau, kuma wani rukunin mutum biyar za su karɓi na su a mako mai zuwa. Ya zuwa yanzu, an raba babura sama da 50 ga ma’aikatan."
- Zayyanu Umar-Aliero
Meyasa gwamna ya raba babura a Kebbi?
Kwamishinan ya bayyana rabon baburan a matsayin wani ɓangare na ƙudrin Gwamna Nasir Idris na samar da yanayi mai kyau domin gudanar da aiki.
"In dai batun aiki ne, gwamna ba ya muna wariya, ba ya la'akari da babba ko ƙarami ko inda mutum ya fito. Yana tabbatar da cewa duk nau'ikan ma'aikata suna jin cewa ana yabawa kan aikin da suke yi.
- Zayyanu Umar-Aliero
Gwamna Nasir ya raba muƙamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya jawo matasa ƴan jam'iyyar APC ya gwangwaje su da muƙamai.
Gwamna Nasir Idria ya ba matasa 200 na jam'iyyar APC waɗanda suka ƙunshi maza da mata muƙaman masu taimaka masa na musamman.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng